Amurka ta sake jefa wa mutanen Gaza tallafin abinci

Jirgin ya jefa gorunan ruwan sha sama da dubu 23 a yankin da ke dauke da masu tsananin bukata.

Amurka ta sake jefa wa mutanen Gaza tallafin abinci

Wani jirgin saman dakon kaya na Sojin Amurka ya jefa jakunkunan kayan abinci 41,400  ga ’yan gudun hijira a Arewacin Gaza.

Kazalika, jirgin ya jefa gorunan ruwan sha sama da dubu 23 a yankin da ke ɗauke da masu tsananin buƙata.

Wannan shi ne karo na biyar da Amurka ta raba kayan agajin abinci ta sama ga ’yan gudun hijiran Gaza da Isra’ila ke ci gaba da yi wa luguden wuta.

Raba kayan ta wannan hanya ya biyo bayan jinkirta amincewa da kai kayan ta kasa da Isra’ila ta yi, lamarin da ya sa Amurka da sauran ƙasashen duniya suka karkata wajen kai agajin ta sama domin gaggauta kai ɗauki ga ’yan gudun hijira.

Kafofin watsa labarai sun ruwaito cewa a ranar Juma’ar da ta gabata ne wani jirgin saman rabon irin wannan kayan agaji ya kashe mutane 5 tare da jikkata wasu mutum 2 a wani sansani ’yan gudun hijira a Arewacin Gaza.

Ana fargabar cewa jirgin ya yi wannan ta’asa yayin da yake jefo kayan a wani sansani, inda Isra’ila ta yi zargin cewa jirgin na Amurka ne, amma daga bisani Amurkar ta fito ta musanta hakan.

Wani ma’aikacin lafiya a babban asibitin Gaza ya ce wani jirgin saman jin-ƙai ya hallaka mutane biyar tare da jikkata 10 a Arewacin ƙasar yayin jefo kayan agajin ta sama ga wani sansanin ’yan gudun hijira.

Bayanai sun ce Amurka da Jordan na daga cikin ƙasashen da ke kai kayan agaji ta sama a yankin Arewacin Gaza da dubban mutane ke fuskantar mawuyacin hali, dalilin da ya sa Isra’ila ta yi zargin cewa jirgin Amurka ne ya yi wannan ta’adi.

A ƙofar banɗakin Gidan Yarin Kuje nake kwana — Ɗan zanga-zanga

An ceto jaririyar da ’yar aikin gida ta sace a Edo

An ceto mutum 58 da aka sace a Kaduna

Sarkin Zazzau ya naɗa sabbin hakimai 7