Amurka ta sake kai farmaki kan mayakan Houthi a Yemen
Iran ta ce wannan harin tsokanar fada ne da zai mamaye yankin Gabas ta Tsakiya.
Amurka ta sake kaddamar da wani sabon farmaki a Yemen biyo bayan shan alwashi da Joe Biden ya yi na kare jiragen ruwan dakon kaya da ke ratsa tekun Bahar Maliya.
Jaridar New York Times ta ruwaito cewa, Amurka ta kai hare-haren ne a kan wasu wurare fiye da 12 a kasar Yeman da ke karkashin ikon mayakan Houthi masu samun goyon bayan Iran.
- Yadda mata ke fin maza ɗaukaka a finafinai a Nijeriya
- Sojoji sun kashe kwamandojin ISWAP uku a Borno
Harin na zuwa ne kwana guda bayan makamancinsa da Amurka da takwararta Birtaniya suka kaddamar a kan jiragen yakin dakarun Houthi da ke kan tekun, lamarin da ke kara jefa fargabar ci gaba da yaduwar rikicin Isra’ila a Gabas ta Tsakiya.
Harin na sama da na ruwa da Amurka ke jagoranta martani ne ga sama da dozin biyu na hare-haren mayakan Houthi da suka kaddamar da makamai masu linzami kan jigilar kayayyaki a tekun Bahar Maliya tun a watan Nuwamba.
Bayanai sun ce mayakan na Houthi na ci gaba da jadadda barazanar su ta hana kaya shiga Isra’ila ta tekun, matukar bata dakatar da ruwan wutar da take yi a Gaza ba.
Ganau sun shaida wa manema labarai cewa kasashen sun yi amfani da bama-bamai wajen kai wa jiragen mayakan Houthi hari a kan gabar tekun Maliya ta Hodeidah da kuma gab da sansanin soji na Hajja.
Tun a jiya Juma’a ne dubban mutane suka gudanar da zanga-zanga a birane da dama na kasar Yemen, don nuna bacin rai dangane da hare-haren da jiragen yakin Birtaniya da Amurka suka kai wa cibiyoyin mayakan kungiyar Houthi da ke rike da madafan iko a kasar.
Tuni dai Iran ta yi Allah wadai da wannan hari tana mai kwatanta shi da tsokanar fadan da zai mamaye yankin Gabas ta Tsakiya.