Amurka ta sake tura sojojinta Iraki
Sakataren Tsaron Amurka Chuck Hagel ya ce dakarun kasarsa kimanin 130 ne suka isa Iraki domin taimakawa wajen kawar da barazanar mayaka masu da’awar kafa daular Musulunci.Yayin da yake wata ganawa da dakarun kasar a jihar California shekaranjiya Laraba, Mista Hagel ya bayyana cewa sojojin za su bayar da cikakken bayani kan sahihin abun da […]
Sakataren Tsaron Amurka Chuck Hagel ya ce dakarun kasarsa kimanin 130 ne suka isa Iraki domin taimakawa wajen kawar da barazanar mayaka masu da’awar kafa daular Musulunci.
Yayin da yake wata ganawa da dakarun kasar a jihar California shekaranjiya Laraba, Mista Hagel ya bayyana cewa sojojin za su bayar da cikakken bayani kan sahihin abun da ke faruwa a yankin da ‘yan gwagwarmayar suka karbe.
A cewarsa sojojin za su taimaka wa fararen hula kusan dubu 30 da suka makale a tsaunin Sinjar da mayakan suka yi wa kawanya. Da yake mayar da martani kan dalilin da ya sa Amurka ta aike da dakarun, ya ce “hakan ba sabun abu ba ne, Amurka ta saba taimakawa Iraki,” inji shi.
Hukumar sojin Amurkan ta kuma bayyana cewa an kai wasu hare-hare ta hanyar yin amfani da jirage marasa matuka kan wuraren da ‘yan gwagwamayar. Haka kuma wani babban jirgin dakon kaya na sojin Amurka ya kammala jefa karin kayayyakin agaji da kuma ruwa ga ’yan gudun hijra.
Har ila yau, Shugaba Barack Obama ya yi marhabin da nada Haidar al-Abadi a matsayin sabon Firaministan Iraki.
Shugaban ya ce ya yi magana da Mista Abadin tare da bukatar shi da ya kafa gwamnati da za ta hada dukkannin wakilan kabilu da darikun kasar. Kodayake Firaminista mai barin gado Nouri al-Maliki bai amince da nadin ba, inda yace hakan ya sabawa tanade-tanaden kundin tsarin mulkin kasar.