‘Amurka ta sha alwashin ganin an sako ’yan matan Chibok’

kasar Amurka ta ce za ta yi dukkannin abin da ya dace don ganin an sako ’yan matan garin Chibok wadanda ’yan kungiyar Boko Haram suka sace a cikin watan Afrilun da ya wuce. An samu wannan tabbacin ne lokacin da jami’in Hulda da ’Yan jarida daga ofishin jakadancin Amurka a Najeriya Sean J. Maclntosh […]

‘Amurka ta sha alwashin ganin an sako ’yan matan Chibok’
‘Amurka ta sha alwashin ganin an sako ’yan matan Chibok’

kasar Amurka ta ce za ta yi dukkannin abin da ya dace don ganin an sako ’yan matan garin Chibok wadanda ’yan kungiyar Boko Haram suka sace a cikin watan Afrilun da ya wuce.

An samu wannan tabbacin ne lokacin da jami’in Hulda da ’Yan jarida daga ofishin jakadancin Amurka a Najeriya Sean J. Maclntosh ya kai ziyara ofishin jaridun Daily Trust da ke Abuja, ranar Talata.
Ya ce: “Kubuto da ’yan matan wani da abu ne da gwamnatin Amurka tafi ba fifiko.”
Akan batun yaki da ’yan kungiyar Boko Haram, ya ce Amurka na taimakawa Najeriya kuma suna musayar bayanai sirri a tsakaninsu.