Amurka ta soki shugabannin Afrika kan gaza yakar ta’addanci
Kasar Amurka ta soki shugabannin kasashen Yammacin Afirka na yankin Sahel da rashin yin abin da ya dace wajen yaki da masu tsatstsauran ra’ayin addinin Musulunci. Mataimakiyar Jadakan Amurka a Majalisar Dinkin Duniya, Cherith Norman Chalet ce ta bayyana haka a gaban Kwamitin Tsaro na Majalisar, inda ta ce kasar Mali ba ta yi wani […]
Kasar Amurka ta soki shugabannin kasashen Yammacin Afirka na yankin Sahel da rashin yin abin da ya dace wajen yaki da masu tsatstsauran ra’ayin addinin Musulunci.
Mataimakiyar Jadakan Amurka a Majalisar Dinkin Duniya, Cherith Norman Chalet ce ta bayyana haka a gaban Kwamitin Tsaro na Majalisar, inda ta ce kasar Mali ba ta yi wani abin a zo a gani ba wajen aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya.
Yayin gudanar da wani taro na musamman kan halin da ake ciki a Yankin Sahel, Jakadiyar Amurka Cherith Norman ta shaida wa Kwamitin Sulhun cewa shugabannin kasashen da ke yankin ba sa daukar matakan da suka dace wajen yakin da ke gabansu.
Cherith ta ce daukar matakan soji kawai ba za su magance matsalar da ta haifar da tashin hankali a yankin ba, inda ta ce Amurka ta bada taimakon da ya kai Dala biliyan biyar da rabi daga shekarar 2017 zuwa 2018 domin samar da tsaro a Afirka ta Yamma.
Jami’ar ta bayyana kasar Mali a matsayin wadda ta kasa samun ci gaba wajen samar da zaman lafiya duk da yarjejeniyar zaman lafiyar da aka kulla a shekarar 2015.
Norman ta ce yana da muhimmanci kasashen da ke Afirka ta Yamma su bai wa kowanne bangare damar fada-a-ji kan shugabancin kasashensu da kuma raba arzikin kasa.
….Kasashen sun bukaci a hada kai a yaki ta’addanci
A wajen taron kasashen yankin Sahel na G5 a Yamai Babban Birnin Jamhuriyar Nijar, shugabannin kasashen suka bukaci da a hada kai a matakin yanki da kasa da kasa don yaki da ta’addanci.
Tun farko dai an shirya yin taron ne a Burkina Faso amma sakamakon kashe sojojin Nijar 71 a yankin Tillaberi da ke Yammacin kasar ya sanya aka mayar da shi zuwa Yamai inda shugabannin kasashen Mali, Chadi, Muritaniya, Burkina Faso da Nijar suka halarta.
Shugaban Burkina Faso, Roch Marc Christian Kabore da ke jagorantar kasashen biyar ya tunatar kan muhimmanci hadin kai a tsakanin kasashen sakamakon yawaitar kai hare-hare da ake yi.
Kabore ya ce sai an samun hadin kan kasashen nasu da kasashen duniya sannan za a iya shawo kan matsalar ta’addanci a yankin da hare-haren da ake kai masa ke tsananta. Dole ne kasashen G5 su yi amfani da cikakken karfin da suke da shi.
Shugaban Nijar Muhammad Yusuf ya ce harin da aka kai musu ba wai sojoji kawai ya shafa ba har da fararen hula da shugabannin gargajiya. Ya ce suna bukatar karfafar junansu domin yaki da ta’addanci a kasashensu.
A makon jiya ne wani bangare na Kungiyar IS ya kai hari a wani sansanin soji a yammacin Nijar wanda ya salwantar da rayukan sojojin kasar 71.