Amurka ta yi musayar soja daya da kwamandojin Taliban biyar

kasar Amurka ta yi musayar sojanta daya da wasu shugabannin Taliban biyar da ke tsare a kurkukun kare kukanka na Guantanamo Bayan.Sojan Amurkan mai suna Saje Bowe Bergdahl mai shekara 28 ya kasance a hannun kungiyar Taliban na tsawon shekara biyar, bayan kama shi a ranar 30 ga Yunin shekarar 2009.Shugabannin na Taliban da suka […]

Amurka ta yi musayar soja daya da kwamandojin Taliban biyar
Amurka ta yi musayar soja daya da kwamandojin Taliban biyar

kasar Amurka ta yi musayar sojanta daya da wasu shugabannin Taliban biyar da ke tsare a kurkukun kare kukanka na Guantanamo Bayan.
Sojan Amurkan mai suna Saje Bowe Bergdahl mai shekara 28 ya kasance a hannun kungiyar Taliban na tsawon shekara biyar, bayan kama shi a ranar 30 ga Yunin shekarar 2009.
Shugabannin na Taliban da suka hada da Mohammad Fazl da Mullah Norullah Noori da Mohammed Nabi da Khairulla Khaikhwa da Abdul Hak Wasik sun isa katar a ranar Lahadin da ta gabata.
Shugaban Taliban Mullah Omar ya bayyana sako su a matsayin “babbar nasara.”
Mullah Omar, ya ce “Ina mika sakon taya murna ga daukacin Musulmin kasar Afghanistan da dukkan mujahidai da kuma iyalan fursunonin kan wannan babbar nasara.”
“Kuma ina godiya ga gwamnatin katar musamman Sarki Sheikh Tamim bin Hamad (Al Thani), wanda ya sadaukar da kansa wajen sako wadannan shugabanni tare da shirya tarbarsu,” inji Mullah Omar.
Kwamandojin na Taliban suna cikin manyan jami’an gwamnatin Taliban da Amurka ta kora a shekarar 2001, Fazl ya kasance Mataimakin Ministan Tsaro yayin da Noori yake Gwamnan yankin Balkh.
A ranar Asabar ne Taliban ta mika Bergdahl ga sojojin Amurka a wani yanki da ke gabashin Afghanistan a kusa da iyakar Pakistan, kuma jami’an Amurka sun ce yana cikin koshin lafiya.