Amurka tana amfani da addini wajen raba kan Musulmi – Ayatollah
Shugaban Addinin a kasar Iran Ayatollah Seyyed Ali Khamenei ya ce kasar Amurka tana amfani da bambance-bambancen addini da na kabilanci wajen haddasa takaddama tsakanin mutane. Shugaban ya bayyana hakan ne ranar Litinin lokacin taron tunawa da shahidan kurdawan Peshmerga. Ya ce amma makiyanmu sun kasa samun nasara wajen amfani da bambancin addini da kabilanci […]
Shugaban Addinin a kasar Iran Ayatollah Seyyed Ali Khamenei ya ce kasar Amurka tana amfani da bambance-bambancen addini da na kabilanci wajen haddasa takaddama tsakanin mutane.
Shugaban ya bayyana hakan ne ranar Litinin lokacin taron tunawa da shahidan kurdawan Peshmerga. Ya ce amma makiyanmu sun kasa samun nasara wajen amfani da bambancin addini da kabilanci domin tada zaune tsaye a yankunan kurdawa da ke Iran.
Jagoran ya ci gaba da cewa: “Lokacin juyin juya halin Musuluncin kasar a shekarar 1979, masu adawa da shi sun ta kokarin haddasa rashin kwanciyar hankali a yankin, amma zukatan kurdawa da malamansu tana tare da akidojin juyin juya halin.”
Daga nan ya jaddada cewa “makiyi ba ya kwanciya” kuma yana amfani da tsaro da farfagandan da kudi wajen jawo rashin jituwa tsakanin Musulmi. “A wurinsu ba wani bambanci tsakanin ’yan Shi’a da mabiya akidar Sunnah,” inji shi.
Ya ce abin takaicin shi ne wasu jama’a na fada wa tarkon makiyanmu. Jagoran ya ce: “Yakamata magoya bayanmu su kula sosai, wanda saboda yadda yake bin akidar Sunnah sau da kafa, hakan ya sanya shi takalar mabiya Shi’a, to wannan ba ya biyayya ga akidarsa da kuma addinin Musulunci. Hakazalika, wanda saboda biyayyarsa ga akidar Shi’a ya takali mabiya akidar Sunnah, wannan shi ma ba shi da madogara a addini,” inji shi.