Amurka za ta ba ’yan tawayen Siriya ofishin jakadanci a Washington

Gwamnatin Amurka ta ce ta aminta da kungiyar hadakar ’yan tawayen  Siriya wato (Syrian National Coalition SNC) inda ta yi alkawarin gina masu ofishin jakadanci a biranen Newyork da Washington. Sanarwar ta zo ne bayan ziyarar Jagorar ‘yan tawayen Ahmad Jarba ta farko a  kasar Amurka tun bayan kafa kungiyar ’yan tawayen a shekarar 2012. […]

Amurka za ta ba ’yan tawayen Siriya ofishin jakadanci a Washington
Amurka za ta ba ’yan tawayen Siriya ofishin jakadanci a Washington

Gwamnatin Amurka ta ce ta aminta da kungiyar hadakar ’yan tawayen  Siriya wato (Syrian National Coalition SNC) inda ta yi alkawarin gina masu ofishin jakadanci a biranen Newyork da Washington.
Sanarwar ta zo ne bayan ziyarar Jagorar ‘yan tawayen Ahmad Jarba ta farko a  kasar Amurka tun bayan kafa kungiyar ’yan tawayen a shekarar 2012. A lokacin ziyarar da ya kai ranar Litinin da ta gabata, ya gana da Sakataren Harkokin Wajen Amurka John Kerry inda ya yi alkawarin karin taimakon
Dala miliyan 27 ga ’yan tawayen a fatan Amurka na ganin sun hanbarar da gwamnatin Shugaba Bashar al-Assad
Mataimakiyar Mai Magana da Yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka Marie Harf ta ce za su karfafa wa ’yan tawayen gwiwa da gina ofishin jakadancin wanda hakan zai taimaka masu wajen gudanar da harkokinsu na hada-hadar kudi da kuma taimaka masu wajen kai wa ga ’yan Siriya mazauna Amurka.
Jarba ya bayyana cewa wannan lokacin mai mahimmanci ne ga fafutukarsu ta gina sabuwar Siriya, da amincewa da ita a matsayin kasa da kuma dangatakarta da ’yan Siriya  mazauna Amurka. Ya kara da cewa “wannan matakin cikas ne ga gwamnatin Shugaba Assad.
Sai dai kuma  gwamnatin Assad na ci gaba da samun nasara kan mayakan ’yan tawayen. Har-ila yau, gwamnatin ta bayyana aniyarta ta na gudanar da zabe a ranar uku ga watan gobe, wanda kuma masawa ke hasashen cewa Shugaba Assad ne zai lashe. Amma tun kafin zuwan ranar zaben, Amurka ta ce  “zaben ba shi da sahihanci, kuma na bogi ne”
A watan da ya gabata ne, Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta rufe Ofishin Jakadancin Siriya da ke birnin Washington da kuma wasu kananan ofisoshin jakadanci da ke kasar.
Agajin da Amurkan ke baiwa ’yan tawayen dai ya hada da kayan abinci da magunguna da na’urorin sadarwa da kuma ababan hawa. Sai dai ’yan tawayaen sun so a ce taimakon na Amurka ya hada da jiragen sama da kuma makamai.