Amurka za ta dauki mataki kan Sudan ta Kudu
A shekaranjiya Laraba ne gwamnatin kasar Amurka tace tana kan tattaunawa da sauran manyan kasashen duniya domin sanya takunkumi ga shugabannin Sudan ta Kudu da ke rikici da juna idan har ba su amince da yarjejeniyar samar da zaman lafiya ba, kamar yadda kafar yada labarai ta RFI ya bayyana.Tuni dai Amurka da Birtaniya suka […]
A shekaranjiya Laraba ne gwamnatin kasar Amurka tace tana kan tattaunawa da sauran manyan kasashen duniya domin sanya takunkumi ga shugabannin Sudan ta Kudu da ke rikici da juna idan har ba su amince da yarjejeniyar samar da zaman lafiya ba, kamar yadda kafar yada labarai ta RFI ya bayyana.
Tuni dai Amurka da Birtaniya suka bukaci Majalisar dinkin Duniya ta kakaba wa gwamnatin Sudan ta Kudun takunkumi kan kin amincewa ta sanya hannu ga yarjejeniyar zaman lafiyar da aka kulla ranar Litinin domin kawo karshen tashin hankalin da ake yi a kasar na tsawon shekaru biyu.
Mai bai wa Shugaban Amurka, Barack Obama, shawara kan sha’anin tsaro, Susan Rice ta bayyana a cikin wata sanarwa cewa za su dauki matakin takunkumi idan har ba a amince da yarjejeniyar ba nan da mako biyu.
Shugaban Sudan Salba Kiir ya ki amince da yarjejeniyar a ranar Litinin da shugabannin kasashen Afirka suka gabatar.
kasar Sudan ta Kudu da ta samu ’yanci daga Jamhuriyar Sudan a shekarar 2011, kuma ta fada cikin rikici ne a watan Disambar 2013, bayan Shugaba Kiir ya zargi tsohon mataimakinsa Riek Machar da yunkurin kifar da gwamnatinsa.