Amurka za ta dawo wa Najeriya $954,000 da tsohon Gwamnan Bayelsa ya sace

Za a yi amfani da kudin wajen gina cibiyar lafiya domin amfanin talakawan jihar….

 Amurka za ta dawo wa Najeriya $954,000 da tsohon Gwamnan Bayelsa ya sace

Marigayi Diepreye Alamieyeseigha

Amurka da Najeriya sun rattaba hannu kan yarjejeniyar maido da Dala 954,000, da aka kwato daga hannun tsohon Gwamnan Jihar Bayelsa, marigayi Diepreye Alamieyeseigha, a loakcin da yake rike da jihar.

Jakadiyar Amurka a Najeriya, Mary Leonard tare da Lauyar Gwamnatin Tarayya kuma Babbar Sakatariyar Ma’aikatar Shari’a, Misis Beatrice Jeddy-Agba ne suka sanya hannu kan yarjejeniyar ranar Alhamis a Abuja.

“Kudaden wani bangare ne na Dalar Amurka miliyan daya da tsohon Gwamnan Bayelsa, DSP Alamieyeseigha, ya wasushewa a lokacin da yake gwamna,” in ji Jeddy-Agba.

Ta ce, Gwamnatin Tarayya ta amince a yi amfani da kudin wajen gina cibiyar kula da lafiya a Bayelsa don amfanin al’ummar jihar.

Ta kara da cewa, kudaden da aka kwato sun hada da nawa gidaje da kadarorin da marigayin ya boye a yankunan Maryland da Massachusetts a Amurka.