Amurka za ta kwashe dakarunta fiye da 1,000 daga Nijar

Amurka ta kashe sama da $100m wajen gina sansanin sojin a Agadez inda take amfani da jirage maras matuƙa.

Amurka za ta kwashe dakarunta fiye da 1,000 daga Nijar

Amurka ta amince za ta kwashe dakarunta sama da 1,000 daga sansanin sojin da ke yankin Agadez a Jamhuriyar Nijar.

Mataimakin Sakataren Harkokin Wajen Amurka Kurt Campbell ne ya bayyana haka ranar Juma’a a ganawar da suka yi da Firaiministan Nijar, Ali Mahaman Lamine Zeine a Washington.

Wasu jami’an Gwamnatin Amurka da ba su so a ambaci sunansu ba sun shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters cewa nan da kwanaki kaɗan masu zuwa ɓangarorin biyu za su tattauna a Yamai kan yadda za a tsara ficewar dakarun Amurka daga Nijar.

Amurka ta kashe sama da $100m wajen gina sansanin sojin a yankin Agadez inda take amfani da jirage maras matuƙa wajen yaƙi da ƙungiyoyin ’yan ta’adda da ke addabar yankin Sahel.

A watan jiya ne gwamnatin Nijar ta sanar da yanke hulɗar soji da Amurka, watanni kaɗan bayan dakarun Faransa sama da 1,500 sun kammala ficewa daga ƙasar.

Lamarin ya faru ne kwanaki kaɗan bayan wata tawagar jami’an gwamnatin Amurka, wadda ke ƙarƙashin jagorancin Mataimakiyar Sakataren Harkokin Wajen sashen Afirka, Molly Phee, ta je Nijar don ganawa da shugaban mulkin soji amma hakan ya gagara.

Gwamnatin mulkin sojin Nijar ta zargi jami’an gwamnatin Amurka da rashin bin ƙa’idojin diflomasiyya da kuma ƙin gaya wa gwamnatin sojin ƙasar mutanen da ke cikin tawagar da ta je Nijar.

Sai dai majiyar ta ce gwamnatocin biyu za su ci gaba da gudanar da dangantakar diflomasiyya da ta tattalin arziki.

Sojojin Nijar sun kori Faransa daga ƙasar bayan sun samu rashin jituwa da ƙasar da ta yi musu mulkin mallaka, sakamakon juyin mulkin da suka yi wa Mohamed Bazoum a watan Yulin da ya gabata.

Kazalika sun soke yarjeniyoyi biyu kan harkokin tsaro da ƙasar ta ƙulla da Tarayyar Turai.

A watan Disamban da ya gabata sojojin na Nijar suka ƙulla yarjejeniya da Rasha, inda kuma a makon jiya, sojojin Rasha da sauran ƙwararrun kan aiki soji guda 100 suka isa Yamai domin horar da dakarun ƙasar.