Amurka za ta sayar wa Saudiyya makaman dala biliyan 1.96
Makaman za su taimaka wa Saudiyya wajen kare kanta daga hare-haren jiragen yaƙi marasa matuƙi da makamai masu linzami.
Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta amince da sayar wa Saudiyya makaman kariya daga hare-haren sama da darajarsu ta kai kusan dala biliyan 1.96, domin ƙarfafa tsaron ƙasar a yayin da rikici ke ƙara tsananta a Gabas ta Tsakiya.
A cewar ma’aikatar, makaman za su taimaka wa Saudiyya wajen kare kanta daga hare-haren jiragen yaƙi marasa matuƙi da makamai masu linzami, tare da rage dogaro da tsarin kariya na Patriot wanda yake mai tsadar gaske.
Yarjejeniyar ta ƙunshi makamai kusan 20,000 na Advanced Precision Kill Weapon System (APKWS), da na’urorin harba makamai, ƙananan bama-bamai da injinan rokoki.
Bayanai sun ce kamfanin BAE Systems da ke Jihar New Jersey ta Amurka shi ne zai jagoranci aiwatar da cinikin.
Matakin ya biyo bayan sabon tashin hankali tsakanin Saudiyya da ƙungiyar Houthi ta Yemen, bayan harin makami mai linzami da Houthi ta kai kan filin jirgin saman Abha da ke kudancin Saudiyya a ranar Litinin.
Harin na Houthi ya biyo bayan harin da gwamnatin Yemen ta kai kan filin jirgin saman Sanaa, da nufin dakatar da wani jirgi da ke dawowa daga jana’izar Jagoran Addini na Iran, wanda ya ɗauko tawagar Houthi, harin da ƙungiyar ta yi zargin Saudiyya da hannu a harin.
A wani mataki na daban, Amurka ta kuma amince da yiwuwar sayar wa Kuwait kayan tallafin jiragen C-17 da sauran kayan aiki masu alaƙa da su, da darajarsu ta kai dala miliyan 484.