Amurka za ta tura dakaru don yakar IS ta kasa
kasar Amurka ta ce tana duba yiwuwar aike wa da dakaru ta kasa don yakar mayakan kungiyar kasar Musulunci ta (IS) da ke kasar Iraki, kamar yadda manyan jami’an sojin kasar suka bayyana shekaranjiya Laraba.A ranar Talata ne Janar Martin Dempsey, kuma shugaban hafsoshin kasar ya ce akwai yiwuwar zai umarci dakarun kasar da su […]
kasar Amurka ta ce tana duba yiwuwar aike wa da dakaru ta kasa don yakar mayakan kungiyar kasar Musulunci ta (IS) da ke kasar Iraki, kamar yadda manyan jami’an sojin kasar suka bayyana shekaranjiya Laraba.
A ranar Talata ne Janar Martin Dempsey, kuma shugaban hafsoshin kasar ya ce akwai yiwuwar zai umarci dakarun kasar da su sa kaimi, ta yadda za su agaza wa dakarun Iraki lokacin da aka kai manyan farmaki ta sama, musamman ma lokacin artabun kwace arewacin birnin Mosul daga mayakan IS. Kodayake Janar Dempsey din ya ce yana sane da shirin Shugaba Barack Obama na cewa ba zai yi amfani da sojin kasa ba, kai-tsaye. “Amma ya shaida mini da na dinga tuntubar shi akai-akai, don ko da bukatar hakan ta taso” inji shi.
Har ila yau, Sakataren Tsaron Amurka Chuck Hagel, ya bayyana wa Kwamitin Dakarun kasar na Majalisar Dattawa, shirin gwamnatin Obama na kai hari ta sama ga mayaka a Siriya da kuma kai farmaki a mafakar ’yan kungiyar IS, da cibiyoyin da kuma sansanoninta.
Sai dai, janar din ya bayyana wa kwamitin cewa farmakin ba zai yi kama da irin wanda ya biyo bayan mamayar da Amurka ta jagoranta a shekarar 2003 a Iraki ba.
Jiragen saman yakin Amurka sun fara kai farmaki ga mayakan IS a arewacin kasar Iraki tun farkon watan Agustan bana. Kodayake, a kwana-kwana nan, jiragen sun kai hari a Kudu-maso-Yammacin birnin Bagadaza a karon farko, a wani mataki na fadada hare-haren da ake kai wa ’yan IS.