Amurka za ta yaki IS ta hanyar Intanet

A ranar Litinin da ta gabata ne kasar Amurka ta bayyana bukatar yakar kungiyar gwagwarmaya kafa Daular Musuluci ta (IS) ta hanyar sadarwa ta Intanet don kawo karshen farfagandar da take yadawa.  John Allen, wani janar din Amurka ne da ya halarci taron wanda hadakar kawayen da ke yaki da kungiyar suka yi a kasar […]

Amurka za ta yaki IS ta hanyar Intanet
Amurka za ta yaki IS ta hanyar Intanet

A ranar Litinin da ta gabata ne kasar Amurka ta bayyana bukatar yakar kungiyar gwagwarmaya kafa Daular Musuluci ta (IS) ta hanyar sadarwa ta Intanet don kawo karshen farfagandar da take yadawa. 

John Allen, wani janar din Amurka ne da ya halarci taron wanda hadakar kawayen da ke yaki da kungiyar suka yi a kasar Kuwait, wanda kuma ya zargi kungiyar IS da rura wutar ayyukan ta’asa ta hanyar Intanet, inda take ba da horo ga jama’ar da ba su ji ba, ba su gani ba.
Ya ce: “Ta hanyar da kawai za mu iya kawo karshen wannan shi ne mu yaki hakan ta Intanet, ta hanyar rusa hujjojin da ke cikin sakonnin da suke aikawa ga matasa masu rauni. Da wannan ne kawai za mu ci galaba kan kungiyar,” inji shi.
Mista Allen wanda yake jagorantar yaki da kungiyar IS ya zanta ne da wakilai kasashe kawaye, ciki har Birtaniya da Bahrain da Masar da Faransa da Iraki da Jordan da Saudiyya da sauransu.
kungiyar IS ta karbe iko da galibin yankunan kasar Siriya da Iraki, inda kuma ta ayyana kafa Daular Musulunci tare da amfani da hanyar Intanet wajen yaka manufofinta. Tana yada faya-fayan bidiyo da buga mujallar kungiyar. Kuma wasu daga cikin bidiyon suna nuna irin ayyukan ta’asar da take aikatawa ciki har da sare kan ’yan jaridar Amurka biyu da ma’aikatan agajin Birtaniya biyu.
kungiyar tana da dimbin magoya baya a shafukan sada zumunta na Intanet wanda ya zama wani wuri na shigar da mayakan kasashen waje cikin kungiyar. Wannan ya sa gwamnatocin kasashen yamma suke ci gaba da bayyana damuwa saboda yadda ake karin samun mutane daga kasashen Turai da Amurka suke nufa kasar Siriya don zama mayakan IS, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito.