An ƙaddamar da dashen bishiyoyi 200,000 a Dambatta

Garin na daga wuraren da suke fama da zaizayar ƙasa a ƙaramar hukumar.

An ƙaddamar da dashen bishiyoyi 200,000 a Dambatta

Hukumar Yaƙi da Kwararar Hamada da Zaizayar Ƙasa (National Agency for the Great Green Wall), ta ƙaddamar da dashen bishiyoyi 200,000 a garin Fagwalawa Dashi da ke ƙaramar hukumar Dambatta a Jihar Kano.

An ƙaddamar da dashen ne da nufin daƙile kwararar rairayin hamada da zaizayar ƙasa tare da gurɓacewar ƙasar noma da al’ummar yankin ke fama da ita.

Daraktan hukumar a nan Kano, Auwal Yusuf, ya ce kamar yadda suka saba duk shekara su kan yi dashen bishiyoyi domin daƙile kwararar hamada tare da kare al’ummar da ke rayuwa a yankunan.

“Yau mun zo Jihar Kano, garin Fagwalawa Dashi da ke ƙaramar hukumar Dambatta inda muke shuke-shuken bishiyoyi wanda muke yi duk shekara saboda kwararar hamada.”

Kazalika, ya ce za su yi dashen ne a faɗin fili mai girman hekta 176 wanda ya ƙunshi bishiyoyi 200,000.

Bishiyoyin da aka dasa sun haɗa da barbejiya, bishiyar kuka, tsamiya, adu’a, ɗorawa da kuma maɗaci.

A cewar daraktan, dasa irin waɗannan bishiyoyi na da matuƙar alfanu duba da yadda bishiyoyin na daga cikin waɗanda suke cikin barazanar ƙarewa a sassan jihar.

Da yake jawabi, mai unguwar Garin Fagwalawa, Malam Isah Shua’ibu, ya gode wa hukumar kan yadda suka zaɓi yankinsa don yin dashen bishiyoyin.

Kazalika, ya ce garin yana fama da matsalar zaizayar ƙasa da kwararar hamada.

Sannan ya ƙara da cewa dasa irin waɗannan bishiyoyi zai taimaka musu wajen samun magunguna na gargajiya.

“Gaskiya ina ganin tun da aka zo aka yi wannan dashe in shaa Allah za a samu sauƙin zaizayar ƙasa, kuma ko shekarun baya da aka yi mana wannan dashen mun samu sauƙi sosai.

“An yi mana dashen na kilomita biyar da kilomita 10, sannan ga shi an dasa abubuwan da ba mu da su irin su adu’a, ɗinya wanda suna da muhimmanci a wajenmu ko daga magunguna da muke ɗiba,” a cewarsa.

Kazalika, ko’odinatan hukumar, Ahmad Mukhtar, ya jaddada muhimmancin wannan dashe da cewa waɗannan bishiyoyin galibinsu na gargajiya ne, wanda suka fara ƙarancin samu.

Ya ce garin Dambatta ya shafi wuraren da suke fama da  arazanar rairayin hamada, zaizayar ƙasa da rashin ingancin ƙasar noma.

 

Ga hotunan yadda dashen bishiyoyin ya gudana:

Isra’ila ta sake fitar da sabon sharaɗin tsagaita wuta a Gaza

Mutanen da gobarar tankar mai ta kashe sun kai 86 a Neja

DSS ta kama ’yan Boko Haram 10 a Osun

Mutum 60 sun mutu a fashewar tankar mai a Neja