An ƙaddamar da littafin magance matsalolin auren dole a Idi-Araba
Littafin mai taken ‘Wanda nake so zan aura’ Garba Ahmed Idris, haifaffen Idi-Araba ya wallafa domin warware matsalolin auren dole.
A ranar Asabar da ta gabata ce al’ummar garin Idi-Araba da ke Ƙaramar Hukumar Munshin a Jihar Legas suka yi bikin ƙaddamar da littafin da ɗaya daga cikin Hausawa haifaffun garin ya wallafa.
Littafin mai taken ‘Wanda nake so zan aura’ Garba Ahmed Idris, haifaffen Idi-Araba ya wallafa domin warware matsalolin auren dole, inganta al’adun ƙasar Hausa da na Afirka, da kuma bai wa masu karatu nishaɗi tare da ɗebe masu kewa.
- Yadda fasinjoji suka ceto yara 5 da ‘wata ‘yar sanda’ ta sato daga Sakkwato
- Cutar ƙyanda ta laƙume rayuka 42 a Adamawa
Sarkin Hausawan Idi Araba Alhaji Hassan Auyo na ɗaya daga cikin manyan garin, Alhaji Ali Aware ne suka jagoranci ƙaddamar da littafin, wanda jama’a da dama maza da mata, daga ciki da wajen unguwar suka halarta.
A zantawarsa da Aminiya bayan ƙaddamar da littafin, Alhaji Ali Aware, ɗaya daga cikin dattawan garin Idi -Araba, da Legas da Ogun baki ɗaya, ya ce ɗaukacin al’ummar garin Idi-Araba na fari ciki tare da alfahari da aikin da mawallafin littafin, Garba Ahmad Idris ya yi.
Ya ce hakan ne ya sanya al’ummar garin suka yi cincirindo a lokacin ƙaddamar da littafi.
Wannan aiki ne da zai daɗa ɗaukaka garin Idi-Araba a idon duniya, don haka ina kira ga sauran masu tasowa a wannan gari su yi koyi da mawallafin littafin, su yi karatu su nemi ilimi su kuma yi aiki da shi domin su amfana kuma su amfanar.
“Su guji shaye-shaye da zaman banza, ina kuma kira ga al’ummar garin Idi-Araba da Nijeriya baki ɗaya su nemi wannan littafi su karanta don sun fa’idantu da baiwar da Allah Ya yi wa marubucin littafin,” in ji shi.
A ɓangaren Sarkin Hausawan Idi-Araba Alhaji Hassan Auyo ya shaida wa Aminiya cewa an ƙaddamar da littafin a daidai lokacin da ake buƙatarsa.
Ya ce littafi ne da zai magance matsalolin auren dole da zamantakewa, don haka suna alfahari da ɗansu, wanda ya wallafa littafin domin magance matsalolin da suka addabi al’umma.
“Wannan littafi ne da ya kamata a bai wa muhimmanci a kuma karanta domin a fa’idantu da hukimomin mawallafin littafin,” in ji shi.
Farfesa Joseph Babashola Osoba, Farfesa a fannin harsuna, wanda ya halarci ƙaddamar da littafin, ya shaida wa Aminiya cewa littafin ya zo a lokacin da ake buƙatarsa.
“Domin yana ƙunshe da al’adun ƙasashen Afirka, kasancewar mawallafin ya samu ne daga manyan kabilun Nijeriya biyu kuma a unguwar Idi-Araba.
“Ka ga mahaifinsa Bahaushe ne daga Jihar Kano, mahaifiyarsa kuma Bayarabiya ce, to ka ga ya tattaro al’adun mahaifiyarsa da na mahaifinsa.
“To fatanmu shi ne tunda littafin an wallafa shi ne da harshen Ingilishi, ya kamata a fassara shi zuwa manyan harsunan kasar nan, wato Hausa da Yarbanci da Ibo, domin a fadada yawan wadanda za su amfana da shi, domin mu ma harsunanmu na Afirka suna da tasiri da alfanu kwarai wajen isar da sako,” in ji shi.
Mawallafin littafin, Garba Ahmed Idris ya shaida wa Aminiya cewa ya wallafa littafin ne domin bunkasa al’adun Hausawa da na Afirka cikin harshen Ingilishi.
Ya ce babban kalubalen da marubuta ko mawallafan littattafai suke fuskanta a wannan lokaci shi ne karancin karatu daga bangaren jama’a. Don haka ya yi fatan al’umma za su karanta littafin domin su anfana.
“A wannan lokaci karatu ya yi karanci, har a tsakanin masu ilimi, ba sa son karatun littattafai, kuma a ganina ka karanta abu ya fi ka kalla ko ka saurara, don haka ina fatan jama’a za su nemi wannan littafi su karanta kuma su amfana,” in ji shi.