An ƙaddamar wa ’yan kasuwa sabon tsarin biyan haraji a Gombe
Hukumar ta ce ta fito da sabbin hanyoyin da za su sauƙaƙa wa ‘yan kasuwa wajen biyan harajinsu.
![An ƙaddamar wa ’yan kasuwa sabon tsarin biyan haraji a Gombe An ƙaddamar wa ’yan kasuwa sabon tsarin biyan haraji a Gombe](https://aminiya.ng/wp-content/uploads/2025/02/IMG-20250206-WA0055.jpg)
A ƙoƙarin bunƙasa tattalin arziƙin Jihar Gombe, Hukumar Tattara Kuɗaɗen Shiga ta jihar, ƙarƙashin jagorancin Hajiya Aisha Adamu, ta ƙaddamar wa ’yan kasuwa sabon tsarin biyan haraji.
An ƙaddamar da tsarin ne a sakatariyar Ƙungiyar ’Yan Kasuwa da ke cikin babbar kasuwar Gombe.
- Majalisa na son ƙirƙiro sabbin jihohi 31 a Najeriya
- An tsinci gawar Ɗan Majalisar da aka yi garkuwa a jajibirin Kirsimeti
Hajiya Aisha ta jinjina wa haɗin kan ’yan kasuwa, musamman, Alhaji Sanusi Abdullahi Mai Rediyo.
Ta ce kuɗaɗen haraji suna da muhimmanci wajen aiwatar da ayyukan raya ƙasa don amfanin al’umma.
Ta yi kira ga ’yan kasuwa da su dage wajen biyan harajinsu na shekara-shekara, wanda kowane mai shago zai biya sau ɗaya kawai.
Hajiya Aisha ta kuma bayyana cewa an samar da hanyoyin biyan haraji masu sauƙi, ciki har da ofisoshin haraji, Intanet, da kuma hedikwatar Hukumar Tattara Kuɗaɗen Shiga.
Shugaban Ƙungiyar ’Yan Kasuwa, Alhaji Sanusi Mai Rediyo, ya tabbatar da cikakken goyon bayansu ga wannan tsari.
Shi ma Sakataren Tsare-tsare na ƙungiyar, Alhaji Sabo Coca Cola, ya jaddada muhimmancin haɗin kai domin cimma burin bunƙasa tattalin arziƙin jihar.
Sabon tsarin biyan harajin zai taimaka wajen ƙara kuɗaɗen shiga na cikin gida tare da inganta ayyukan ci gaba a Jihar Gombe.