An ƙayyade kuɗin tsayawa takara a zaɓen ƙananan hukumomin Kano 

Za a yi gwajin ƙwaya kafin a ba mutum damar tsayawa takara.

An ƙayyade kuɗin tsayawa takara a zaɓen ƙananan hukumomin Kano 

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf

Hukumar Zaɓen Kano (KANSIEC) ta ƙayyade kuɗin sayen fom ɗin tsayawa takara a zaɓen ƙananan hukumomin jihar da za a gudanar a bana.

Shugaban hukumar zaɓen, Farfesa Sani Lawal Malumfashi ne ya sanar da hakan ne a yayin bayyana jadawali da ƙa’idojin shiga zaɓen a wani taron manema labarai da hukumar ta gudanar a Kano a ranar Alhamis.

A yayin taron, hukumar zaɓen ta sanar da cewa duk mai son tsayawa takarar shugaban ƙaramar hukuma a zaɓen to zai sayi fom a kan naira miliyan 10.

Yayin da ɗan takarar kansila kuma kuɗin fom ɗinsa ya kama naira miliyan biyar a cewar Farfesa Malumfashi.

Haka kuma, daga cikin ƙa’idojin shiga zaɓen dole ne ɗan takarar kujerar shugaban karamar hukuma ya kasance shekarun haihuwarsa sun kai 30 ko fiye, yayin da ɗan takarar kansila tilas ne ya kasance ya kai shekara 25 zuwa sama.

Kazalika, Farfesa Malumfashi ya ce sai an yi wa kowanne ɗan takara a zaɓen ƙananan hukumomin jihar da za a yi gwajin ƙwaya kafin a ba shi damar tsayawa takara.

Aminiya ta ruwaito cewa, hukumar zaɓe wadda ta yi gargadi kan gujewa duk wani lamari da zai tayar da hargitsi, ta ce za a buɗe ƙofar soma yaƙin neman zaɓe daga ranar 6 ga watan Satumba sannan a rufe a ranar 31 ga watan Oktoban bana.

Farfesa Malumfashi ya nanata cewa ba za su lamunci duk nau’i na rashawa ba kuma duk wanda aka samu da yunƙurin bayarwa ko karɓar cin hanci za a tona masa asiri sannan ya fuskanci hukuncin da aka tanadar.

Za a gudanar da zaɓen ƙananan hukumomin jihar ne a ranar 30 ga watan Nuwambar 2024.