An ɗage ranar dawowar makarantu daga hutu a Kano
An ɗage ranar komawar makarantun Kano daga hutun ƙarshen shekarar karatu har sai abin da hali ya yi
Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Kano ta ɗage ranar komawar makarantun firamare da sakandare daga hutu har sai abin da hali ya yi.
Ma’aikatar ta ce ta ɗage lokacin komawa hutun makarantun ne saboda wasu “dalilai na gaggawa”, amma ba ta yi ƙarin bayani ba.
Sai dai ta ce matakin zai inganta yanayin makarantun da tsarin ilimi a jihar.
Ma’aikatar ilimin, a cikin wata sanarwa da Daraktan Wayar da Kan Jama’a, Balarabe Kiru, ya sanya wa hannu, ta ce nan gaba za ta sanar da ranar buɗe makarantun.
- Sojojin 196 sun ajiye aiki a Najeriya
- NAJERIYA A YAU: ‘Karin Farashin Mai Ya Fara Tilasta ‘Yan Najeriya Ajiye Aiki’
An ɗage lokacin komawa hutun makarantun jihar Kano ne bayan gwamnatin jihar Edo ta sanar da irin hakan.
Amma a nata ɓangaren, Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Edo ta ce ta ɗauki matakin ne sakamakon tashin farashin mai da na kayan masarufi da suka shafi ƙarfin aljihun iyayen yara.
A ranar Litinin, 9 ga Satumba, 2024 ne dai yawancin makarantun firamare da sakandare za su koma aji daga hutu domin fara sabuwar shekarar karatu ta 2024/2025.
Ma’aikatar ilimin, a cikin wata sanarwa da daraktan wayar da kan jama’a, Balarabe Kiru, ya sanya wa hannu ta ce nan gaba za ta sanar fa ranar buɗe makarantun.