An ɗage Shari’ar Tsohon Al’kalin Da Ya Doki Makauniya Matar Aure

Kotu ta ɗage sauraron ƙarar da aka kai wani tsohon alƙalin kotun Musulunci kan cin zarafin wata matar aure makauniya a Zariya.

An ɗage Shari’ar Tsohon Al’kalin Da Ya Doki Makauniya Matar Aure

Kotu ta ɗage sauraron ƙarar da aka kai wani tsohon alƙalin kotun Musulunci kan cin zarafin wata matar aure makauniya a Zariya.

An gurfanar da tsohon Al’kalin Babban Kotun Shari’ar Musulunci Mahmoud Shehu me bisa zargin keta iyaka da nuna karfi da kuma cin zarafin wata matar auren.

Kotun Majistare da ke ta Zariya ta dage shari’ar ce zuwa ranar 11 ga watan Nuwaba 2024.

Dan sanda mai gabatar da ƙara, Sufeto Adamu Abubakar ya shaida wa kotu cewa a ranar 6 ga watan Satumba mijin matar ne ya kai rahoto ofishin ’yan danda da ke Tudun Wada Zariya cewar Mahmoud Shehu ya rufe babar Kofar Gidan da suke haya tare da shi inda ya bi matarsa Sa’adiya har ɗakinta ya buge ta da sandar lema sai da aka kai ta asibiti.

Magidancin ya bayyana wa alkali cewa tsohon alƙalin ya kuma bugi waɗanda ke zama da ita su biyu.

Lauyoyin wadda ake ƙara SM Abubakar da Ibrahim B. Ahmed sun nemi kotu ta sanya masu wata rana saboda ɓangaren masu ƙara su samar masu da takardun bayanan tuhume-tuhumen da ake ma wanda suke kare wa domin su fahimci inda aka sa gaba.

Mai Shari’a Majistare Lukman Sidi ya amince da ranar 11 ga watan Nuwamba 2024 a matsayin ranar da za a ci gaba da sauraren karar.

Da yake bayyana takaicinsa a game da abin ya faru, Shugaban Ƙungiyar Nakasassu reshen Jihar Kaduna, Barista Ibrahim Sani Zubairu ya ce sun halarci zaman kotunne domin a yi komai a gabansu kasancewar wanda ake zargin tsohon masanin shari’ar Musulunci ne.

Lakurawa sun kashe ma’aikatan kamfanin Airtel 3 a Kebbi

Matashi ya kashe mahaifiyarsa don yin tsafi a Kuros Riba

DSS ta ceto mutum 4 da aka sace a Sakkwato

2025: Wutar lantarkin Najeriya ta ɗauke gaba ɗaya