An ɗauke wutar lantarki a faɗin Najeriya
Wutar lantarki ta dauƙe gaba ɗaya a faɗin Najeriya a safiyar Alhamis.
Wutar lantarki ta dauƙe gaba ɗaya a faɗin Najeriya a safiyar Alhamis a sakamakon durkushewar babban layin lantarkin kasar.
Hakan na zuwa ne makonni kaɗan bayan kamfanin samar da wutar lantarki na Najeriya (TCN) ya sanar da cikarsa shekara guda ba tare da babban layinsa na lantarki ya samu ɗaukewar wutar gaba ɗaya ba, kamar yadda aka saba a ƙasar.
- An haramta wa jiragen ruwa tafiyar dare a Taraba
- Asian Cup: Mata za su yi alkalanci a Gasar Kofin Maza a Qatar
Wata sanarwa da kamfanin rarraba wutar lantarki na Enugu (EEDC) ya fitar a safiyar ta ce wutar ta fara ɗaukewa ne da misalin ƙarfe 12:40 na dare ne.
Sakamakon haka, “duk tashoshinmu ba su da wutar lantarki da za su raba a jihohin Abia, Anambra, Ebonyi, Enugu da Imo.”
Aminiya ta gano cewa ƙarfin wutar lantarkin kasar ya ragu zuwa megawatt 273 daga cikin biyu daga cikin cibiyoyinta 27.