An ɗaure malami shekara 20 kan sukar gwamnati a Saudiyya

Hukuncin na zuwa ne bayan sukar da ya yi wa gwamnatin ƙasar a shoshiyal midiya.

An ɗaure malami shekara 20 kan sukar gwamnati a Saudiyya

Saudiyya ta yanke wa wani malami Asaad al-Ghamdi mai shekara 47 hukuncin ɗaurin shekara 20 a gidan yari saboda sukar gwamnati a shafukan sada zumunta.

An kama shi a watan Nuwamban 2022 a birnin Jeddah, kuma aka yanke masa hukunci a ranar 29 ga Mayu a wata kotu ta musamman, inda aka zarge shi da ta’addanci.

Takardun kotu sun nuna cewa an tuhumi Ghamdi da “ƙalubalantar addini da adalcin Sarki da Yarima” da “wallafa jita-jita da labarun ƙarya.”

Shaidun da aka gabatar sun haɗa da rubuce-rubucen da ya suka soki ayyukan ‘Vision 2030’ da nuna alhininsa ga mutuwar ɗan gwagwarmaya Abdallah al-Hamed.

Lamarin Ghamdi ya yi kama da na ɗan uwansa Mohammad, wanda aka yanke wa hukuncin kisa a bara saboda yaɗa wasu rubuce-rubuce a shafukan sada zumunta.

Ɗan uwansu na uku, Saeed, wanda malamin addini ne da ke gudun hijira, ya yi Allah-wadai da hukuncin, inda ya ce babu komai game da tuhume-tuhumen face zalunci.

A cikin ’yan shekarun nan, kotunan Saudiyya sun yanke hukuncin ɗaurin shekaru masu tsawo ga mutane da dama saboda rubuce-rubuce a shafukan sada zumunta, ciki har da Nourah al-Qahtani da aka yanke wa hukuncin shekara 45 da Salma al-Shehab da aka yanke wa hukuncin ɗaurin shekara 34.

Akwai Manahel al-Otaibi, wadda aka yanke wa hukuncin shekara 11 saboda ƙalubalantar dokokin Saudiyya game da sanya sanya abaya ga mata.

Kamfanin da ya daina aka ba kwangilar titin Abuja-Kaduna

NAJERIYA A YAU: Yadda Kuɗin Kujera Yake Neman Hana Maniyyata Sauke Farali

NCC ta amince wa kamfanonin sadarwa ƙara kuɗin kira da data

Amurka jinsin mace da namiji kaɗai ta sani a hukumance — Trump