Satar allon kabari ya kai matsahi kurkuku a Kano

Kotun ta yanke masa hukuncin ɗaurin wata shida tare da bulala

Satar allon kabari ya kai matsahi kurkuku a Kano

Wata makabarta a Kano

Kotun Muslunci ta ɗaure wani matashi mai shekaru 25 a gidan yari tare da yi masa bulala kan laifin satar allon shaidar a kabari a wata maƙabarta a Jihar Kano.

Kotun ta ba da umarnin yanke hukuncin kisa ƙeyar matashin zuwa kurkuku ne bayan da ya amsa laifin sace allunan kabari na ƙarfe guda 15 a makabartar.

Daga nan alkalin kotun, Malam Umar Lawal-Abubakar, ya yanke masa hukuncin daurin wata shida a gidan yari tare da umarnin yi masa bulala 30.

Tun da farko mai gabatar da ƙara  Insfekta Abdullahi Wada, ya shaida wa alƙalin cewa a ranar Talata ne aka kai ƙarar matashin a ofishin ’yan sanda da ke unguwar Dala.

An kai ƙarar matashin ne da cewa ya shiga cikin maƙabarta ya sace allunan kabari shaida na karfe guda akalla 15. (NAN)