An ɗaure mutum 2 kan damfarar Dantata da tsohon minista

Kotun ta samu mutane biyun da laifin damfarar hamshaƙin attajirin da kuma tsohon minista.

An ɗaure mutum 2 kan damfarar Dantata da tsohon minista

Wata Kotun Majistare da ke Gyadi-Gyadi a Jihar Kano, ta ɗaure wasu mutum biyu, kan damfarar hamshaƙin attajirin nan, Alhaji Aminu Dantata da kuma tsohon minista, Abdullahi Tijjani Gwarzo.

Mutanen sun haɗa da Bukar Galadima da Suleiman Ahmed, kuma kotun ta same su da laifin yunƙurin aikata damfara.

Mutanen biyu sun haɗa baki, inda suka karɓi Naira miliyan biyar daga hannun Dantata da Naira miliyan ɗaya daga hannun Gwarzo.

Ɗaya daga cikinsu ya yi kama da tsohon minista, Injiniya Abba Gama, inda ya yi amfani da wannan damar na cewar ba shi da lafiya, ya kuma nemi tallafi a wajen Dantata.

Dantata, ya ba shi Naira miliyan biyar, tare da tunanin cewa tsohon ministan ne.

Bayan gano an damfare shi, Dantata ya kai Hukumar Karɓar Koke-Koke da Yaƙi da Cin Hanci ta Jihar Kano.

Bayan gudanar da bincike, hukumar ta yi nasarar kama Galadima da Ahmed.

Alƙalin kotun, Umma Sani Kurawa, ta same su da laifin haɗa baki da kuma aikata rashin gaskiya.

An yanke musu hukuncin ɗaurin wata shida ko kuma biyan tarar Naira 30,000, da ƙarin ɗaurin wata uku ko biyan Naira 20,000.

Kazalika, kotun ta sake yanke musu hukuncin ɗaurin wata shida ko biyan tarar Naira 20,000 saboda aikata rashin gaskiya.

Kotun ta kuma umarce su da su biya Naira miliyan biyar da suka damfari Dantata ko kuma su shafe shekara biyu a gidan yari.

Lauyan hukumar yaƙi da cin hancin, Zahraddeen Kofar Mata, ya ce sun gano Naira miliyan ɗaya da aka damfari Gwarzo, duk da cewar bai shigar da ƙara ba.

Ya bayyana cewa an same su da laifi ƙarƙashin sashe na 129 (8) na dokar Jihar Kano ta 2019.