An ɗaure shi a kurkuku kan damfarar tsohuwar matarsa

Kotun Musulunci ta yanke wa wani mutum hukuncin ɗaurin wata biyu kan damfarar tsohuwar matarsa.

An ɗaure shi a kurkuku kan damfarar tsohuwar matarsa

Kotu

Kotun Musulunci ta yanke wa wani mutum hukuncin ɗaurin wata biyu kan damfarar tsohuwar matarsa.

Kotun da ke zamanta a ’Yan Alluna a Ƙaramar Hukumar Fagge, ta yanke hukuncin ne bayan samun sa da laifin ba wa tsohuwar matarsa rasit ɗin bogi na kuɗin abincin ɗansu.

A yayin gurfanar da wanda ake zargin ya masa cewa ya je wani shago ne aka buga masa rasit ɗin bogi na Naira dubu hamsin da ya ba wa tsohuwar matar tasa.

Ya shaida wa kotun cewa a unguwar Mandawari aka buga masa rasit ɗin bogi na Naira dubu hamsin.

Mai Shari’a Khadi Nasir Abdullahi Muhammad, yaba yanke masa hukuncin ɗaurin wata uku ko biyan tarar Naira dubu hamsin.

Ya kuma ba da umarnin yi masa bulala 10.

Tinubu zai tafi Faransa daga nan ya zarce Habasha

NAHCON ta tsawaita wa’adin biyan kuɗin Hajjin bana

Jami’ar ABU da ke Zariya ta yi sabon shugaba

An soma rigimar haraji tsakanin China da Amurka