An ɗaure shi wata 9 kan doya ƙwara 2

yanke wa wani mutum hukuncin zaman gidan yari na wata tara kan laifin satar doya ƙwara biyu.

An ɗaure shi wata 9 kan doya ƙwara 2

Kotu ta yanke wa wani mutum hukuncin zaman gidan yari na wata tara kan laifin satar doya ƙwara biyu.

A ranar Alhamis Kotun Majistare da ke Kafanchan, Jihar Kaduna, ta yanke masa hukuncin, bayan ya amsa cewa yunwa ce ta sa shi satar doyan, ya kuma nemi sassauci.

Alkalin kotun, Michael Bawa, ya ba wa mutumin zaɓin biyan tarar N50,000 ko zaman gidan yari na wata tara.

Tun da farko jami’in Sibil Difens mai gabatar da ƙara, Marcus Audu, ya shaida wa kotun cewa, a ranar 15 ga watan Agusta ne mutumin ya shiga gonar mai ƙara, Alice Daniel, ya saci doya ƙwara biyu a yankin Zonkwa.

(NAN)

An kama bokaye 2 kan zargin yi wa shugaban Zambiya asiri

Kirsimeti: FRSC ta aike jami’ai 1,539 zuwa Kano

Gwamnatin Kano na shirin tara harajin 80bn a 2025

Kirsimeti: Zulum ya ɗauki nauyin jigilar fasinjoji 710 zuwa garuruwansu

Tags