An ɗaure ‘yan Najeriya kan takardun auren bogi 2,000 a Birtaniya
Sun dai yi wa ‘yan Najeriya takardar zamba ta Tarayyar Turai EU Settlement Scheme ga ‘yan Najeriya daga watan Maris 2019 zuwa Mayun a bara,
An ɗaure wasu rukunin ’yan Najeriya huɗu shekaru 13 a gidan yari kan lafin ba da takardun aure na bogi sama da 2,000 ga masu neman zama a Burtaniya ba bisa ƙa’ida ba.
Waɗanda aka ɗaure sun haɗa da: Abraham Alade Olarotimi Onifade, mai shekara 41 da Abayomi Aderinsoye Shodipo mai shekara 38, da Nosimot Mojisola Gbadamosi mai shekara 31 da Adekunle Kabir mai shekara 54.
- Lalube cikin duhu Gwamnatin Tinubu take yi —Atiku
- HOTUNA: ’Yan Shi’a da ’yan sanda suka kama bayan rikicin Abuja
ma’aikatar cikin gida ta Birtaniya ta ce mutanen sun yi wa ’yan Najeriya takardar bogi ta Tarayyar Turai EU Settlement Scheme daga watan Maris 2019 zuwa Mayun a bara.
Sukan kuma ba da takarddun shaidar auren gargajiya ta Najeriya ta bogi da sauransu don tallafa wa don taimaka musu su ci gaba da zama a ƙasar.
Wani bincike da Ofishin ya gudanar ya gano wasu takardun auren bogi fiye da 2,000 a hannunsu.
Jami’in kula da shige-da-fice na Ofishin Cikin, Gida Paul Moran ya ce: “Wannan gungu ya yi fice wajen cin zarafin iyakokinmu kuma an gurfanar da su a gaban kotu.”