An aike da gawar Bajapaniya ta gidan waya – Rahoto

Jami’an binciken laifukan kisa a kasar Japan, sun fara binciken yadda aka aike da sakon gawar wata malamar jinya, ta akwatin gidan waya, inda aka rubuta wa wasikar ’yar tsana. Gawar matar da ake kira da Rika Okada, an same ta a wani firji da aka kulle a birnin Tokyo. Masu binciken sun samu akwati […]

An aike da gawar Bajapaniya ta gidan waya – Rahoto
An aike da gawar Bajapaniya ta gidan waya – Rahoto

Jami’an binciken laifukan kisa a kasar Japan, sun fara binciken yadda aka aike da sakon gawar wata malamar jinya, ta akwatin gidan waya, inda aka rubuta wa wasikar ’yar tsana. Gawar matar da ake kira da Rika Okada, an same ta a wani firji da aka kulle a birnin Tokyo. Masu binciken sun samu akwati mai tsawon mita biyu, wanda aka dauko shi daga Kudancin birnin Osaka, kamar yadda rahotanni suka bayyana.
An lullube akwatin da takardar mai dauke da kan sarki, inda aka yi wani rubutu da haruffan Japananci, mai ma’anar ’yar tsana. An yi tafiyar kilomita 400 zu8wa Tokyo, sannan an biya kudin aikewa da sakon da sunan mamaciyar Okada. Sannan kudin sakon an biya su ne da katin hadar-hadar jkudinta (credit card).
Wannan gawa, ta mace mai shekara 29, wadda ta bace tun a cikin watan Maris, yana da raunuka fiye da 12, kamar yadda kafafen yada labaran kasar suka bayyana, amma babu wasu alamu da suka nuna ta yi kokarin kare kanta.
Jami’an  ’yan sanda sun ki bai wa manema labarai cikakken bayani, amma rahotanni na nuni da cewa, ‘wata kawar marigayiyar, wadda suka yi makarantar elemantare tare, ta yi amfani da fasfo dinta ta fita daga birnin Tokyo, a farkon wannan watan.’
Wannan abokiyar karatunta, wadda ba a ambaci sunanta ba, ana tunanin tana zaune tare da wata ’yar kasar Sin, tsararta.
daukacin wadannan mata dai sun tashi daga filin jirgin saman Haneda da ke birnin Tokyo, a jirgi guda zuwa birnin Shangai da ke kasar Sin.
Kafin Okada ta bace, ta rubuta wani sako a shafin sadarwarta na Facebook, cewa, .za ta ziyarci kawarta da suka dade ba su gana da juna ba.’