An aike masu zanga-zanga 632 gidan yari a Kano
Wasu daga cikin waɗanda ake tuhumar sun ƙi amsa laifin da ake zargin su da aikatawa.
Kotun ta fi da gidanka, ta aike mutum 632 da ake zargi da tayar da tarzoma a lokacin zanga-zangar matsin rayuwa da ta gudana a Jihar Kano.
An gabatar da zaman kotun ne a harabar hedikwatar rundunar ‘yan sandan jihar da ke Bompai a jihar.
Bayan da masu gabatar da ƙara ƙarƙashin jagorancin Barista Salisu Tahir, suka karanta wa waɗanda ake tuhumar wasu daga cikinsu sun amsa laifin da ake zargin su da shi.
A gefe guda wasu daga cikinsu sun musanta sun musanta aikata laifin; ciki har da lalata dukiyoyin jama’a.
Alƙalan kotunan sun bayar da umarnin tsare waɗanda ake tuhumar a gidan gyaran hali tare da ɗage shari’ar zuwa ranar 19 ga watan Agusta, 2024.
Yayin da yake zantawa da manema labarai, Kwamishinan Shari’a na Jihar Kano, Barista Isah Dederi, ya bayyana cewa Gwamnatin Jihar ce, ta kafa kotun tafi da gidanka guda uku da niyyar gurfanar da waɗanda ake zargin.
Kazalika, ya ce za su nazarci ƙunshin tuhumar da ake yi wa waɗanda aka gurfanar kafin zaman kotun na gaba.
Idan ba a manta ba, tashin hankali da aka samu yayin zanga-zangar ne ,ya sanya gwamnatin jihar sanya dokar hana fita ta sa’o’i 24, kafin daga bisani ta sassauta dokar.