An aiwatar da hukuncin kisa a Jordan

Gwamnatin kasar Jordan ta zartar da hukuncin kisa kan masu tada kayar baya biyu da ake tsare da su a kasar. Hakan dai wani martani ne ga kisan da mayakan kungiyar IS suka yi wa matukin jirgi saman nan dan kasar.daya daga cikinsu mai suna Sajida al-Rishawi ‘yar kunar bakin wake ce, wadda IS suka […]

An aiwatar da hukuncin kisa a Jordan
An aiwatar da hukuncin kisa a Jordan

Gwamnatin kasar Jordan ta zartar da hukuncin kisa kan masu tada kayar baya biyu da ake tsare da su a kasar.

Hakan dai wani martani ne ga kisan da mayakan kungiyar IS suka yi wa matukin jirgi saman nan dan kasar.
daya daga cikinsu mai suna Sajida al-Rishawi ‘yar kunar bakin wake ce, wadda IS suka bukaci ayi musayar ta da matukin jirgin da suke tsare da shi. Gwamnatin Jordan ta sha alwashin daukar fansa akan kisan da mayakan IS suka yi Mu’az al-Kasesbeh a wani hoton bidiyo mai daga hankali da aka nuna yadda suka banka masa wuta alhalin yana raye a cikin wani keji.
Daruruwan mutane ne suka fito akan titunan babban birnin kasar Amman, su na bukatar a dauki fansa kan kisan da aka yi wa Laftanal-Kanar Mua’az al-Kasasbeh. Kuma mahaifinsa na daga cikin wadanda sukai wannan gangamin, sai dai gwamnatin Jordan ta ce jinin sa ba zai tafi a banza ba.
An yankewa al-Rishawi hukuncin kisa ne a shekarar 2005 saboda rawar da ta taka a harin kunar bakin wake da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 60.
Shi ma wani babban jigo na kungiyar al-kaeda Ziyad Karbili da ya kashe wani dan asalin Jordan, an kashe shi a yau.
Mahaifin direban jirgin Safi al-Kasasbeh, ya yi kira ga gwamnatin kasar da ta kara kaimi kada ta tsaya kan aiwatar da hukuncin kisa kawai. Ya ce: “Ina kira da a kawar da kungiyar IS gaba daya daga doran kasa,” inji shi.