An aje gawar Sarkin Peki tsawon shekara 6 saboda sabani tsakanin dangi
Gawar marigayi Togbega Kwadwo na 9 a yankin masarautar Peki a kasar Ghana ta yi shekara 6 a wurin adana gawarwaki da ke wani asibitin gwamnati a Peki, sakamakon sabani tsakanin Majalisar Gargajiyar Peki da iyalan sarauta guda uku a Peki.Takaddama ta barke tsakanin iyalan Nyan Gamangu da Amega Kofi da kuma Tutu Brempong da […]
Gawar marigayi Togbega Kwadwo na 9 a yankin masarautar Peki a kasar Ghana ta yi shekara 6 a wurin adana gawarwaki da ke wani asibitin gwamnati a Peki, sakamakon sabani tsakanin Majalisar Gargajiyar Peki da iyalan sarauta guda uku a Peki.
Takaddama ta barke tsakanin iyalan Nyan Gamangu da Amega Kofi da kuma Tutu Brempong da majalisar masarautar Peki a kan yadda za a binne marigayin tun bayan da ya mutu a shekarar 2009.
Takaddamar baya-baya nan game da wannan lamari a cewar Dihyefiam Peeki wato shugaban masarautar Peki, wanda kuma shi ne shugaban dangin Nyangamangu Togbe katamanto C.C Fittih ta taso ne sakamakon takardar da ya rubuta saboda wadansu da suke neman su binne sarkin.
Dihyefiam ta hannun lauyansa ya rubuta wa ofishin shugaban kasar Ghana da na Minitsan Ma’aikatu wasika, inda ya shaida musu cewa har yanzu ba za a iya binne gawar marigayin ba, saboda ba a bi ka’idojin da suka dace ba.
Ya bukaci hukumomi su tsawata wa mutanen da ba su da wani iko a kan duk wata maganar fitar da gawar daga asibitin Peki.
Lauya Fittih Mista B.B. Bakattah ya nuna cewar mutumin da yake tsaya wa Togbega Dei ya nada shi a matsayin magajin garin Peki a wurin wani taro a Peki Blengo a ranar 18 ga Afrilu 2009 lokacin da lafiyarsa (Togbega Dei) ke ci gaba da tabarbarewa.
“A dalilin haka bayan mutuwar marigayin a watan Mayu, 2009 iyalansa suka shaida wa Togbe Fittih tare da kiransa ya tafi ya dauki gawar. Bayan haka ne wasu suka hada kansu a matsayin kwamitin makoki da binne marigayin. Wannan kwamiti dai be amince da Togbe Fittih a matsayin magajin Peki ko wanda ya dace ya yi binne marigayi sarkin ba, kamar yadda al’ada ta nuna.” Inji Fittih
Ya ce wannan kwamiti na tsaye kan kafafunsa cewar sai ya binne sarkin har suka kai ga tuntubar Daraktan Ma’aikatar kiwon lafiya da ke asibitin gwamnati na Peki yadda za su yi bincike a kan gawar, shi kuma Togbe Fittih ya ce faufau babu wanda ya isa.
A yanzu dai ba a san yaushe za a sulhunta iyalan masarautar Peki da kuma Majalisar masarautar ba.