An tabbatar da Adamu Sufeto Janar na ‘yan Sandan Najeriya

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya amince tare da tabbatar da mukaddashin Sufeto Janar na ‘yan Sandan Najeriya Muhammad Adamu a matsayin sabon Sufeto Janar na ‘Yan Sanda a yau Alhamis. Gwamnan jihar Ekiti Dakta Kayode Fayemi, ne bayyanawa wakilinmu hakan bayan taron da suka yi a fadar shugaban kasar a Abuja. A ranar 15 ga […]

An tabbatar da Adamu Sufeto Janar na ‘yan Sandan Najeriya

Shugaba Buhari yayin da yake yi wa IGP Adamu kwalliyar nadi

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya amince tare da tabbatar da mukaddashin Sufeto Janar na ‘yan Sandan Najeriya Muhammad Adamu a matsayin sabon Sufeto Janar na ‘Yan Sanda a yau Alhamis.

Gwamnan jihar Ekiti Dakta Kayode Fayemi, ne bayyanawa wakilinmu hakan bayan taron da suka yi a fadar shugaban kasar a Abuja.

A ranar 15 ga watan Janairu aka baiwa Muhammad Adamu mukamin mukaddashin Sufeto Janar na ‘yan Sandan Najeriya.