An aurar da mayaka 250 a Iraki

A shekaranjiya Laraba ne aka daura auren mayakan sa-kai ’yan Shi’a su 250, wadanda ke taimaka wa sojoji kasar Iraki wajen yaki da kungiyar gwagwarmaya ta IS a kasar, kamar yadda kafar yada labaran gwamnatin kasar Shafak News ta ruwaito. Bayan an daura auren amaran su 250 da angwayansu 250 ne, sai aka bai wa […]

An aurar da mayaka 250 a Iraki
An aurar da mayaka 250 a Iraki

A shekaranjiya Laraba ne aka daura auren mayakan sa-kai ’yan Shi’a su 250, wadanda ke taimaka wa sojoji kasar Iraki wajen yaki da kungiyar gwagwarmaya ta IS a kasar, kamar yadda kafar yada labaran gwamnatin kasar Shafak News ta ruwaito.

Bayan an daura auren amaran su 250 da angwayansu 250 ne, sai aka bai wa kowanne ango da amarya kyautar talabijin da firji da kuma sauran kayayyakin amfanin gida, kamar yadda wani ministan kasar ya bayyana. Daga nan ya kara da cewa: “Bikin ya samu tallafi daga kamfanonin ciki da wajen kasar Iraki, ciki har da kamfanin jirgin saman kasar.”
Duka angwayen mambobin kungiyar Popular Mobilisation Units ne, wadda take tallafa wa dakarun kasar a yaki da ake da ’yan gwagwarmayan kungiyar IS. Har ila yau, angwayen sun isa wurin daurin auren ne sanye da kakinsu na soji, wani abu da daya daga cikin amaren ta bayyana da “abin sha’awa.”
Mayakan sa-kan dai sun taka muhimmiyar rawa wajen karbo garin Tikrit daga hannun ’yan gwagwarmayan a watan Maris din da ya wuce. Wani abu da wasu suke ganin auren da wata sakayya bisa wancan kokarin nasu.