An ayyana Lakurawa a matsayin ƙungiyar ’yan ta’adda
An haramta wa duk wani mutum ko kuma wata ƙungiya shiga ayyukan ƙungiyar Lakurawa.
Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta ayyana ƙungiyar Lakurawa da ta ɓulla a baya bayan nan a matsayin ƙungiyar ’yan ta’adda.
Wannan hukuncin zai bai wa sojojin ƙasar damar amfani da ƙarfi wurin daƙile barazanar da ƙungiyar ke yi a arewa maso yammacin ƙasar.
- Bello Turji na neman miƙa wuya ga sojoji —Janar Musa
- Matashi ya maƙure mahaifinsa har lahira saboda babur
Alƙali James Omotosho ne ya ayyana ƙungiyar a matsayin ta ta’addanci a wani hukunci da ya yanke a ranar Alhamis, inda ya haramta wa duk wani mutum ko kuma ƙungiya shiga ayyukan ƙungiyar.
Hakan dai na ƙunshe cikin wata sanarwa bayar da tabbaci da Ofishin Ministan Shari’ar Nijeriya, Lateef Fagbemi ya fitar a ranar Juma’a.
Tuni dama Nijeriyar ke yakar ƙungiyoyin da ke ɗauke da makamai da dama da suka haɗa da Boko Haram da reshenta na ƙungiyar IS da ke yammacin Afirka da kuma wasu ƙungiyoyin ’yan bindiga da dama.
Ɓullar ƙungiyar Lakurawa da ta fi tasiri a jihohin Kebbi da Sakkwato da ke arewa maso yammacin Najeriya, ya ƙara ta’azzara matsalar rashin tsaro a arewacin ƙasar.
An zargi ƙungiyar da kai hari a watan Nuwamba a Jihar Kebbi wanda ya yi sanadin mutuwar mutane aƙalla goma sha biyar tare da jikkata wasu da dama bayan sace dabbobi.
Ko a makonni biyu da suka gabata sojoji sun bindige ’yan ƙungiyar Lakurawa aƙalla shida har lahira tare da ƙwato makaman ɓata-garin a Jihar Sakkwato.
Haka kuma, a makon da ya ganata ne ’yan sanda suka kama wasu mutane uku da suka kai musu cin hanci domin hana binciken mayaƙan Lakurawa da aka kama a Jihar Kebbi.