An ayyana N70,000 sabon albashi mafi ƙanƙanta a Jigawa

Gwamnatin ta ce zuwa yanzu ba a ƙayyade haƙiƙanin lokacin da zai soma aiki ba.

An ayyana N70,000 sabon albashi mafi ƙanƙanta a Jigawa

Gwamnan Jigawa, Malam Umar Namadi, ya amince da Naira dubu 70 a matsayin sabon albashin ma’aikata mafi ƙanƙanta a faɗin jihar.

Kwamishinan Labarai, Matasa, Wasanni da Al’adu, Sagir Musa ne ya sanar da hakan yayin zantawarsa da manema labarai ranar Asabar a birnin Dutse.

Ya bayyana cewa, Gwamna Namadi ya ayyana matakin ne a ranar Juma’a bayan karɓar rahoton kwamitin sabon albashi mafi ƙaranci da Shugaban Ma’aikatan Jihar, Muhammad Dagacire ya jagoranta.

“Ina mai farin cikin sanar da cewa Gwamna Umar Namadi a jiya (Juma’a) ya ba da tabbacin aiwatar da sabon albashi mafi ƙanƙanta kamar yadda Gwamnatin Tarayya ta buƙata.

“Wannan matakin na zuwa ne bayan karɓar shawarwari da rahoton kwamitin da aka ɗora wa alhakin nazari kan sabon albashin ma’aikata mafi ƙanƙanta a Jihar Jigawa.”

Sai dai Kwamishinan ya ƙara da cewa abin da ya rage a yanzu shi ne kammala shirye-shiryen aiwatar da sabon tsarin biyan albashin mafi ƙaranci da Gwamnan ya aminta da shi.

Kazalika, Kwamishinan wanda ya ba da tabbacin cewa sabon albashin mafi ƙanƙanta zai fara aiki nan ba da jimawa ba, ya ce zuwa yanzu ba a ƙayyade haƙiƙanin lokacin da zai soma aiki ba.

Ana iya tuna cewa a bayan nan ne Gwamnatin Jigawa, ta yi watsi da jita-jitar da ake yi cewar Gwamna Namadi ya amince da sabon mafi ƙarancin albashi na Naira 70,000.

Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Sakataren Gwamnatin Jihar, Malam Bala Ibrahim ya fitar.

A cewarsa, labarin ba shi da tushe domin kwamitin da da gwamnatin ta kafa kan mafi ƙarancin albashi bai kammala haɗa rahotonsa ba.

Saboda haka, gwamnatin ta kafa sabon kwamitin da zai binciki tushen jita-jitar, da kuma dalilin da ya sa aka yaɗa ta.

Kwamitin zai kasance ƙarƙashin jagorancin Babban Lauyan Jihar kuma Kwamishinan Shari’a, Barista Bello Abdulkadir Fanini.

Sauran mambobin kwamitin sun haɗa da Kwamishinan Watsa Labarai, Sagir Musa Ahmed, Kwamishinan Lafiya, Dokta Muhammad Abdullahi Kainuwa, Babban Sakataren Tsare-Tsare da Ayyuka, Muhammad Yahaya Jabo, da Babban Sakataren REPA, Abba Mustapha Yola.

An bai wa kwamitin mako biyu don kammala bincikensa tare da gabatar da shi ga gwamnan jihar.

Dangane da hakan ne kuma Gwamna Namadi ya dakatar da mai ba shi shawara kan albashi da fansho, Alhaji Bashir Ado Kazaure, har zuwa lokacin da kwamitin zai kammala bincikensa.

Buni ya amince da N70,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi

Sarkin Beli ya rasu bayan shafe shekara 91 a kan mulki

Rashin aiki ya ƙaru zuwa kashi 4.3 a Najeriya — NBS

Mahara sun kashe mutane 30 a hare-haren Benuwe