An ayyana ranar soma jigilar maniyyatan Jigawa

Jihar Jigawa ta kammala kusan kashi 70 cikin 100 na shirye-shiryenta, inda aka riga aka raba jakunkunan alhazai da sauran kayayyakin buƙata.

An ayyana ranar soma jigilar maniyyatan Jigawa

Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Jigawa ta sanar da cewa za ta fara jigilar maniyyata aikin Hajjin bana na 2026 zuwa Saudiyya a ranar 4 ga watan Mayu.

Darakta Janar na hukumar, Ahmad Umar Labbo, ne ya bayyana hakan a wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar dangane da kammala shirye-shiryen ƙarshe gabanin fara jigilar.

Ya ce tuni jihar ta kammala kusan kashi 70 cikin 100 na shirye-shiryenta, inda aka riga aka raba jakunkunan alhazai da sauran kayayyakin buƙata, yayin da abin da ya rage shi ne tattara maniyyata a sansani da kammala wasu tsare-tsare.

A nasa ɓangaren, jami’in gudarwa na NAHCON shiyyar Kano, Jigawa da Katsina, Muhammad Umar Kalgo, ya yaba da yadda jihar ta shirya cikin lokaci, yana mai cewa za a gudanar da binciken ƙarshe kafin fara jigilar.

Haka kuma, kamfanin Umza Airline ya tabbatar da cewa jirgi na farko zai tashi a ranar 4 ga Mayu da misalin ƙarfe 8:30 na dare.

Darakta Janar ɗin ya jinjina wa Gwamna Umar Namadi, bisa goyon bayan da yake bai wa shirin, yana mai jaddada cewa hukumar na da ƙudurin ganin an gudanar da aikin Hajjin bana cikin nasara da lumana.