An ayyana zaman makoki na kwana uku bayan kashe mutum 44 a Nijar
Zaman makokin na awa 72 zai fara aiki ne daga ranar Asabar domin girmama waɗanda suka rasu.

Gwamnatin Nijar ta ayyana zaman makoki na kwana uku bayan an kashe fararen hula 44 a kudu maso yammacin ƙasar a wani hari da “yan ta’adda” da ke da alaƙa da ƙungiyar ta’addanci ta Daesh suka kai.
Ma’aikatar harkokin cikin gida ta ƙasar ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar a gidan talabijin na ƙasar a ranar Juma’a.
- An yi wa wata karya tiyatar ceton rai
- Za a hukunta ma’auratan da suka ci zarafin yarinya a kan mangwaro — Zulum
Sanarwar ta ce ‘yan ta’addan sun kashe fararen hular ne a lokacin da suka afka cikin wani masallaci a ƙauyen Fombita da ke Kokorou inda suka far wa masallata.
Ma’aikatar ta yi Allah-wadai da harin inda ta kira shi da hari na “rashin imani” tare da shan alwashin ƙara matsa ƙaimi domin yaƙi da ta’addanci a yankin.
Zaman makokin da gwamnatin ta Nijar ta sanar na awa 72 zai fara aiki ne daga ranar Asabar domin girmama waɗanda suka rasu.
Za a ɗaga tutocin Nijar rabi a faɗin ƙasar, haka kuma za a dakatar da taruka a daidai lokacin da ƙasar ke cikin makoki.
Yankin kudu maso yammacin Jamhuriyar Nijar, musamman yankunan da ke kusa da kan iyaka da Mali da Burkina Faso, na fuskantar tashe-tashen hankula a ‘yan shekarun nan, inda ƙungiyoyi irin su Daesh ke amfani da rashin zaman lafiya wajen kai munanan hare-hare kan ƙauyuka da jami’an tsaro.
Harin dai ya nuna ƙalubalen tsaro da ƙasar da ke yankin Sahel ke fuskanta, duk kuwa da ƙoƙarin da gwamnati da ƙawayenta na ƙasa da ƙasa suke yi na daƙile ayyukan tada ƙayar baya.
Kawo yanzu dai babu wata kungiya da ta ɗauki alhakin kai harin, ko da yake ma’aikatar harkokin cikin gidan ƙasar ta danganta shi da Daesh saboda kasancewar ƙungiyar a yankin.
Hukumomin ƙasar dai sun yi alƙawarin gudanar da cikakken bincike tare da ɗaukar ƙwararan matakai domin gurfanar da waɗanda suka aikata laifin a gaban kuliya.
Kashe-kashen na baya-bayan nan na ƙara yawan asarar rayukan fararen hula a Nijar, inda al’ummomi ke ci gaba da fuskantar barazanar tashe-tashen hankula.