An ba da belin DPO da ake zargi da yi wa mai ’ya’ya biyu fyade a ofishinsa

An bayar da belin Mista Adekunle Awe, jami’in ’yan sandan da  ake zargi da yi wa wata mai ’ya’ya biyu mai suna Idowu Akinwunmi  fyade a ofishinsa da ke unguwar Onikan a Legas.Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Jihar Legas, Madam Ngozi Braide ta bayyana cewa ana ci gaba da bincike kan lamarin don […]

An ba da belin DPO da ake zargi da yi wa mai ’ya’ya biyu fyade a ofishinsa
An ba da belin DPO da ake zargi da yi wa mai ’ya’ya biyu fyade a ofishinsa

An bayar da belin Mista Adekunle Awe, jami’in ’yan sandan da  ake zargi da yi wa wata mai ’ya’ya biyu mai suna Idowu Akinwunmi  fyade a ofishinsa da ke unguwar Onikan a Legas.
Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan Jihar Legas, Madam Ngozi Braide ta bayyana cewa ana ci gaba da bincike kan lamarin don gano gaskiyar abin da ya faru.
Bayan da aka bayar da belin, kuma an yi zargin cewa ya taba fuskantar zargin aikata fyade a baya. Tuni dai Sufeto-Janar na rundunar ’yan sandan Najeriya, Alhaji M. D. Abubakar ya bayar da umarnin a gudanar da bincike kan lamarin.
An kafa kwamitin mutum uku da aka zabo daga sashen hulda da manema labarai da sashen kare hakkin dan Adam da kuma sashen rundunar yaki da masu laifi ta ’yan sanda.
Tuni kwamitin ya shiga aikin bincike gadan-gadan inda ya ziyarci ofishin jami’in dan sandan, inda ake zargin lamarin ya auku tare da gayyatar ’yan sanda da suke bakin aiki lokacin da lamarin ya auku.
Madam Idowu Akinwumi, mai shekara 31, ta zargi DPO Awe da yi mata fyade bayan da ya yi mata barazanar zai kashe ta yayin da take tsare a ofishin ’yan sanda da ke karkashinsa a unguwar Onikan a ranar 15 ga watan Afrilun shekarar da muke ciki.
Madam Idowu, wacce ke sana’ar dafa abinci a kan titin Keffi da ke unguwar Obalende, ta kai karar Mista Awe ofishin ’yan sanda da ke titin Lion Buliding bayan da aka yi mata gwaje-gwaje a asibitin birnin Ikko.
Kodinetan cibiyar gyara aikin dan sanda ta Najeriya (NOPRIN) mai suna Mista Okechukwu Nwanguma ta yaba wa Sufeto-Janar na ’yan sandan kan matakin da ya dauka kan batun.
Ta ce, “Ba don matakin gaggawa da Sufeto-Janar na ’yan sanda ya dauka ba, na bayar da umarnin a gudanar da binciken gaggawa da yanzu maganar ta zama tarihi, kamar yadda irin lamarin ya faru a baya”.
Sai dai DPO Awe ya musanta zargin da Madam Idowu ta yi masa inda ya bayyana cewa sharri ne kawai ta yi masa.