An ba da belin masu zanga-zangar tsadar rayuwa kan naira miliyan 10

Waɗanda ake zargin na iya fuskantar hukuncin kisa idan aka kama su da aikata laifukan da ake tuhumar su.

An ba da belin masu zanga-zangar tsadar rayuwa kan naira miliyan 10

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta bayar da belin mutum 10 da ake tuhuma da cin amanar ƙasa yayin zanga-zanga kan tsadar rayuwa.

Mai Shari’a Emeka Nwite ya ce ya ba da belin maza tara da mace ɗaya, waɗanda ba su amsa tuhumar da ake yi musu ba kan naira miliyan 10 kowannensu.

Waɗanda aka bayar da belin sun haɗa da; Michael Adaramoye da aka fi sani da Lenin; Adeyemi Abayomi, Suleiman Yakubu, Opaluwa Simon, Angel Innocent, Buhari Lawal, Mosiu Sadiq, Bashir Bello, Nuradeen Khakis da Abdusalam Zubairu.

Aminiya ta ruwaito cewa, Gwamnatin Tarayya ta hannun Babban Sufeton ’yan sanda ce ta gurfanar da ababen zargin sakamakon ƙunshin ƙarar da ta shigar mai lamba FHC/ABJ/CR/454/2024 a ranar 30 ga watan Agusta.

Cikin tuhume-tuhumen da ake yi musu har da haɗa baki wajen tunzura sojoji su kifar da gwamnatin Bola Tinubu a zanga-zangar da suka gudanar a watan Agusta.

Sai dai tun da farko masu shigar da ƙara sun nemi kotun ta yi watsi da neman belin a makon da ya gabata.

Waɗanda ake zargin na iya fuskantar hukuncin kisa idan aka kama su da aikata laifukan da ake tuhumar su.

Alƙalin ya ɗage ci gaba da sauraron ƙarar har zuwa ranar 27 ga watan Satumba.

Ana iya tuna cewa, a farkon watan Agustan da ya gabata ne jama’a suka gudanar da zanga-zangar tsadar rayuwa a faɗin Nijeriya.