An ba da belin Yunusa Yellow
An bayar da belin saurayin nan da ake zargin ya sace wata yarinya ‘yar Jihar Bayelsa wato, Yunusa Dahiru, bayan ya shafe wata shida a tsare. Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Yenagoa, babban birnin Jihar Bayelsa ce ta umarci ba da belin saurayin, wanda ake wa lakabi da Yunusa Yellow. Ana zarginsa ne dai […]

An bayar da belin saurayin nan da ake zargin ya sace wata yarinya ‘yar Jihar Bayelsa wato, Yunusa Dahiru, bayan ya shafe wata shida a tsare.
Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Yenagoa, babban birnin Jihar Bayelsa ce ta umarci ba da belin saurayin, wanda ake wa lakabi da Yunusa Yellow.
Ana zarginsa ne dai da sace wata budurwa mai suna, Ese Oruru, sannan ya aure ta ba tare da amincewarta ba, kodayake ya sha musanta zargin. Abin da ya jawo ce-ce-ku-ce a shafukan sada zumunta da muhawara.
Kotun dai ta bayar da belin Yunusa ne bayan ya cika sharudan belin da aka gindaya masa.
Saurayin ya koma Jihar Kano. Kuma za a ci gaba da sauraran shari’arsa ne a ranar 13 ga watan Satumba mai zuwa.