An ba dalibai damar zukar taba a aji don fahimtar darasin da za a koyar

Jami’ar Noma ta Yunan Agricultural Unibersity da ke China ta bai wa dalibai izinin zukar taba a aji don saurin fahimtar darasin da za a koyar da su game da ganyen taba sigari. An yi ta yada hotunan daliban lokacin da suke zaune a aji suna kunna wa tabar wuta suna zukarta a wurin da […]

An ba dalibai damar zukar taba a aji don fahimtar darasin da za a koyar

Jami’ar Noma ta Yunan Agricultural Unibersity da ke China ta bai wa dalibai izinin zukar taba a aji don saurin fahimtar darasin da za a koyar da su game da ganyen taba sigari.

An yi ta yada hotunan daliban lokacin da suke zaune a aji suna kunna wa tabar wuta suna zukarta a wurin da yake kama da aji na wani kwaleji a shafukan Intanet watanni da suka wuce. Sai daga baya ne aka gano cewa daliban jami’a ne ke zukar  taba a aji lokacin daukar darasi kan ganyen taba.

Wadannan sahihan hotuna sun shahara a shafin sada zumunta na China Weibo tun a watan Nuwamba bara. An kuma yi ta yada su a shafukan sada zumunta da sauran kafafen sadarwa don  nuna dalibai na kunna wa  taba wuta suna zuka yayin da wadansu kuma suke daukar hoto, malaminsu yana lura da abin da suke yi. Shan taba ga kananan yara a China ya zama ruwan dare, wadansu kuma na kyamar dabi’ar. Hoton ya razana jama’a da dama ganin yadda a aka rika yada shi a shafukan Intanet duk da Shugaban Sashen Kula da Daliban Jami’ar ya yi bayani a kai.

A cewar Shugaban Harkokin Daliban Jami’ar Yunan, Zhao Zhengdiong, wadannan hotunan da ake ta yadawa an dauke su ne lokacin daukar darasi kan ganyen taba. Malamin da yake koyar da darasin ya kawo nau’o’in taba a cikin ajin kuma ya umarci daliban su zuki tabar don fahimtar darasin da za a koyar da su. Sai dai malamin bai bai wa daliban izinin ci gaba da shan tabar bayan karantar da su darasin ba.

Daliban Jami’ar Yunan sun shiga shafukan Intanet suna mayar da martani ga jama’a game da darasin da aka koya musu da kuma malamin da ya koyar da su kan sukar da ake ta yi musu. Sun ce koyon darasi kan ganyen taba yana da matukar muhimmanci wajen sanin fasahar da ke tattare da zukar taba sigari, kuma ba kullum ake koyar da darasin ba.

Wani dalibi ya ce, ba ana koyar da su shan taba ba ce suna koyon wani ilimi ne na taba sigari.

 

 

 

Hatsarin kwalekwale ya ci rayuka 4 a Borno

Lokacin Soke Tallafin Mai A Najeriya Ya Yi —Dangote

Gwamnatin sojin Burkina Faso ta ce ta sha daƙile yunƙurin hargitsa ƙasar

Za a kai shugaban ’yan sanda kotu kan kudin otel N625m