An ba Dangote da BUA aikin gyaran Titin Abuja-Kaduna

Gwamnatin Najeriya ta ƙwace aikin gyaran Titin Abuja zuwa Kaduna daga hannun kamfanin Julius Berger ta raba wa kamfanonin Ɗangote da BUA

An ba Dangote da BUA aikin gyaran Titin Abuja-Kaduna

Gwamnatin Najeriya ta ƙwace aikin gyaran Titin Abuja zuwa Kaduna daga hannun kamfanin Julius Berger.

A shekarar 2016 gwamnatin tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ta ba kamfanin aikin, amma yanzu bayan shekaru takwas, abin da kamfanin ya kammala bai fi Kashi 27% ba.

Ministan Ayyuka, David Umahi, ya zargi kamfanin Julius Berger da siyasantar da aikin gyaran titin Abuja zuwa Kaduna, inda take amfani da shi wajen tatsar gwamnati mahaukatan kuɗaɗe.

Umahi ya bayyana cewa an raba wa kanfanonin Dangote da BUA ɓangaren aikin da aka ƙwace daga Julius Berger domin su ƙarasa.

Umahi ya ce kamfanonin BUA da Dangote za su gina titin kankare ne, kuma za a biya su ne daga shirin gwamnati na zamiyar kuɗaɗen haraji.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos