An ba iyalan jami’an tsaron da ’yan Ombatse suka kashe Naira miliyan 34

kungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa ta ba da cekin Naira miliyan 34 ga gwamnatin Jihar Nasarawa don tallafa wa iyalan jami’an tsaro da ’yan kungiyar Ombatse suka kashe a kauyen Alakyo a bara. Sakatariyar Gwamnatin Jihar, Hajiya Zainab Abdulmumin ce ta karbi cekin kudin a madadin Gwamnan Jihar Umaru Tanko Al-Makura a Lafiya. Da yake jawabi […]

An ba iyalan jami’an tsaron da ’yan Ombatse suka kashe Naira miliyan 34
An ba iyalan jami’an tsaron da ’yan Ombatse suka kashe Naira miliyan 34

kungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa ta ba da cekin Naira miliyan 34 ga gwamnatin Jihar Nasarawa don tallafa wa iyalan jami’an tsaro da ’yan kungiyar Ombatse suka kashe a kauyen Alakyo a bara.
Sakatariyar Gwamnatin Jihar, Hajiya Zainab Abdulmumin ce ta karbi cekin kudin a madadin Gwamnan Jihar Umaru Tanko Al-Makura a Lafiya.
Da yake jawabi bayan mika cekin, Babban Sakatare mai kula da Sha’anin Mulki da Tsaro na Jihar Neja, Mista Paul Kolo ya ce an ba da kudin ne a matsayin wani bangare na cika alkawarin da kungiyar ta yi watannin baya a lokacin da ta ziyarci jihar don jajanta wa iyalan wadanda aka yi musu kisan gillar.
Ya ce kodayake kungiyar ta yi alkawarin ba da Naira miliyan 100 ne, amma ta yanke shawarar ba da Naira miliyan 34 da aka samu daga wasu gwamnoni a halin yanzu don rage wa iyalan mamatan wahalhalun da suke fuskanta a yanzu.  Ya ce kungiyar za ta cika alkawarin da ta yi na tallafa wa iyalan mamatan.
Hajiya Zainab Abdulmumin ta nuna farin ciki ne ga kungiyar dangane da wannan karamci da kuma yadda kungiyar take tallafa wa al’ummar jihar da ma kasar, musamman wadanda ke fuskantar matsaloli. Ta yi alkawarin isar da sakon ga Gwamna Umaru Tanko Al-Makura wanda ya yi balaguro a halin yanzu. Ta kuma ba da tabbacin cewa za a rarraba kudin yadda ya kamata ga iyalan jami’an tsaron.
Daga nan sai ta bayyana kisan killar da aka yi ga jami’an tsaron a matsayin abin mamaki da rashin imani inda ta ce gwamnatin jihar ta sha alwashin hukunta wadanda ke da hannu cikin lamarin don ya kasance darasi ga masu niyyar yin haka a gaba.
Idan ba a manta ba a ranar 11 ga Mayun bara ce ’yan kungiyar matsafan kabilar Eggon da aka fi sani da Ombatse suka kashe jami’an tsaro sama da 100 a wani kauyen Alakyo inda daga bisani kungiyar gwamnonin Arewa ta ziyarci jihar don jajantawa iyalansu kuma ta yi alkawarin tallafa musu da Naira miliyan 100 don rage musu wahala.