An ba iyalan wadanda suka rasu a rikicin Boko Haram a Jihar Borno tallafi
Gwamnan Jihar Oyo, Sanata Abiola Ajimobi ya mika cakin jimlar Naira miliyan 28 ga iyalan ’yan kasuwar Bodija Ibadan, wadanda suka rasa rayukansu a lokutan da ’yan boko haram suka yi musu kofar rago a Jihar Borno, yayin da suka je fataucin kayan abinci.Gwamnan ya mika cakin kudin ne a harabar kasuwar ta Bodija. ’Yan […]
Gwamnan Jihar Oyo, Sanata Abiola Ajimobi ya mika cakin jimlar Naira miliyan 28 ga iyalan ’yan kasuwar Bodija Ibadan, wadanda suka rasa rayukansu a lokutan da ’yan boko haram suka yi musu kofar rago a Jihar Borno, yayin da suka je fataucin kayan abinci.
Gwamnan ya mika cakin kudin ne a harabar kasuwar ta Bodija. ’Yan kasuwar da suka rasu 14 ne, wadanda gwamnan ya mika wa wakilin iyalin kowane mamaci Naira miliyan biyu a matsayin tallafi.
Gwamnan, wanda ya nuna bakin cikinsa da aukuwar al’amarin, ya bayyana juyayi da tausayinsa ga iyalan mamatan, kuma ya ce, wannan kudi da gwamnati ta ba su, tallafi ne kawai domin ba za a iya mayar da wadanda aka rasa ba, sai dai a dangana al’amarin ga Allah.
Matar daya daga cikin mamatan mai suna Misis Folasade Afolabi, wacce ta yi jawabi a madadin sauran matan, ta nuna farin cikinsu da matakin da gwamnan ya dauka tun daga farkon al’amarin zuwa yanzu, wanda aka rika daukar dawainiyarsu.
Cikin jwabinsa, shugaban kungiyar masu sayar da kayan abinci a birnin Ibadan, Alhaji Olalekan Azeez, ya yi kira ne ga gwamnatin tarayya ta samar da cikakken tsaro, musamman a sashen Arewa, domin tsare rayuka da dukiyar al’ummarta kuma yin hakan zai kawo karshen aukuwar irin wannan barna a nan gaba.