An ba makafi damar amfani da bindiga a Amurka

A Jihar Iowa ta Amurka an bai wa makafi izinin rike bindiga, don haka jami’an tsaro ke ta takaddama kan al’amarin, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na AP ya ruwaito.Rahoton jaridar The Des Moines ya bayyana cewa babu wani tanadi na doka da ya umarci jami’an ’yan sanda su hana wa mutum rike makami bisa […]

An ba makafi damar amfani da bindiga a Amurka
An ba makafi damar amfani da bindiga a Amurka

A Jihar Iowa ta Amurka an bai wa makafi izinin rike bindiga, don haka jami’an tsaro ke ta takaddama kan al’amarin, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na AP ya ruwaito.
Rahoton jaridar The Des Moines ya bayyana cewa babu wani tanadi na doka da ya umarci jami’an ’yan sanda su hana wa mutum rike makami bisa la’akari  nakasarsa. Don haka makafi za su iya neman izinin rike bindiga, bisa la’akari da sauye-sauyen da aka samu a dokokin jihar, wadanda aka fara aiki da su tun a shekarar 2011.
Misis Jane Hudson, Jami’ar Kare Hakkin Nakasassu ta Jihar Iowa, ta bayyana cew ahana makafi rike makafi ya saba wa tanadin da dokar Amurka ta yi wa nakasassu. Ta ce dokokin tarayya sun bijiro da bukatar yin nazarin daidaikun matsaloli kafin ta yi hani a kai.
“Duk da cewa ba za su iya tuka mota ba, ba yana nufin ba za su iya yin harbin abin da suka tunkara ba,” inji ta.

Ban zama Shugaban Kasa don na tara kuɗi ba — Tinubu

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda

‘Yan bindiga sun ƙone gidan mai da motoci 4 a Enugu

Kwalara ta kashe fiye da mutum 300 a Sudan