An ba masu adawa da zanga-zanga Dandalin Eagle Square
Akwai hotunan magoya bayan gwamnati a dandalin Eagles Square ranar Asabar:
Magoya bayan Gwamnatin Tinubu sun hallara a dandalin Eagle Square da ke Abuja, domin nuna adawarsu da zanga-zangar da ake shirin yi kan matsin tattalin arziki a fadin Najeriya.
Sun gudanar da taron ne a Eagle Square ne a yayin da masu shirin zanga-zangar adawa da yunwa da kuma tsadar rayuwa a kasar suka kasa samun izinin amfani da dandalin daga ranar 1 ga watan Agusta.
Taron masu adawa da zanga-zangar da ya gudana a ranar Asabar, ya hado mata daga jihohi 36 da ke fadin Najeriya da kuma Babban Birnin Tarayya, Abuja.
Ga hotunan magoya bayan gwamnati a dandalin Eagles Square ranar Asabar:
- Boko Haram na shirin kutsawa cikin masu zanga-zanga —’Yan sanda
- Zanga-zangar tsadar rayuwa ta barke a Arewa
A ranar Lahadi Daraktan Tsare-tsare na kungiyar Take It Back Movement, wadda ta shirya zanga-zangar, Damilare Adenola, ya sanar a hirarsa da gidan talabijin na Channels TV cewa za su gudanar da zanga-zangar a dandalin Eagle Square ko da gwamnati ba ta amince ba.
Adenola ya ce sun rubuta wa Ministan Abuja, Nyesom Wike, wasikar neman izinin amfani da Eagle Square, mai dauke da kwanan ranar 26 ga Yuli, 2024, kuma an watsa wasikar ta a kafofin sada zumunta.
Sai dai har zuwa ranar Asabar, ministan ya ce bai samu wasikar ba.
Wike ya ce: “Su wa ke son yin zanga-zangar? Idan suna son amfani da Eagle Square, shin a kafofin sada zumunta za su rubuta min?
“Za ku rubuta ne zuwa ga minista, in gani; su wane ne ku; Ke kuke son yi; Kwana nawa kuke so? Nawa za ku biya?
“Dole ku nema ta hanyar da ta dace, ku biya abin da muke kira kudin tsaro, wanda idan aka lalata wurin, za mu dauka daga ciki mu gyara.
“Ba kara-zube muka ba wa mutane ba saboda sun nema. Dole ne ku cika sharuddan.
“Wasu sun riga sun biya kudin Eagle Square, sai daga bisani ku kuka nema; so kuke in soke na farkon saboda kuna son yin zanga-zanga?
“Duk wanda ya riga zuwa shi muke ba wa wuri.
“Ban ce kada mutane su yi zanga-zanga ba, amma ba zanga-zangar tada wa gwamnati zaune tsaye ba.”
Amma a ranar Lahadi, Adenola ya dora laifin jinkirin isar da wasikar a bisa tsaren-tsaren gudanarwa, yana mai jaddada cewa ministan zai samu wasikar ranar Litinin.