An ba matar da ta mayar da tsuntuwa kyautar Naira miliyan daya
Gwamna Abiola Ajimobi na Jihar Oyo ya mika kyautar Naira miliyan daya ga Hajiya Muinatu Agboluaje, wacce ta tsinci Naira miliya biyar a lokacin aikin hajjin bara (2012) ta kai wa jami’an Hukumar Alhazai domin gano ainihin mai kudin a mayar masa. Haka nan, ya bayar da kyautar kujerun hajjin bana da cikakken guzuri ga […]

Gwamna Abiola Ajimobi na Jihar Oyo ya mika kyautar Naira miliyan daya ga Hajiya Muinatu Agboluaje, wacce ta tsinci Naira miliya biyar a lokacin aikin hajjin bara (2012) ta kai wa jami’an Hukumar Alhazai domin gano ainihin mai kudin a mayar masa. Haka nan, ya bayar da kyautar kujerun hajjin bana da cikakken guzuri ga dalibai biyu, Isma’il Ibrahim da Zainab AbdulRazak, wadanda suka lashe gasar karatun Alkur’ani na shekara ta 2013 tsakanin daliban makarantu daban-daban na jihar a Ibadan.
Da yake mika kyautukan a lokacin da yake yi wa mahajjatan bana jawabin ban kwana a sansanin alhazai na Olodo, Gwamnan, wanda yake tare da Sarkin musulmin kasar Yarabawa, Alhaji Abdul’Azeez Arisekola Alao, ya jinjina wa Hajiya Muinatu, wadda ya ce ta cancanci samun fiye da haka. Ya yi kira ga maniyyatan su yi koyi da ita wajen cusa tsoron Allah a zukatansu, wanda zai kai ga amsar addu’o’insu.
Da ya juya ga daliban kuma, Gwamna Ajimobi ya ce, kyakkyawar tarbiyya daga iyaye da imani da Allah da tsoronSa da hakuri suna cikin muhimman abubuwan da suka taimaka musu wajen lashe gasar, saboda haka ya nemi sauran dalibai su kara mayar da hankali domin ganin sun yi nasara a gasar badi, wacce za a yi sabon tanadin raba kyautuka fiye da na bana.
Gwamnan, wanda ya sa a kwashe rukunin mahajjata na farko daga Ibadan zuwa Legas a jirgin sama maimakon motoci, ya ce an yi hakan domin kauce wa matsaloli. Ya bukaci su kasance mutanen kirki masu gaskiya da tsoron Allah a duk lokacin da suke a kasa mai tsarki.
Cikin jawabinsa, Shugaban Hukumar Alhazai ta jihar, Alhaji Taofeek Akewugbagold ya ce jimlar maniyyatan jihar ya tsaya ne a kan 1,227, wadanda hukumarsa ta yi wa kyakkyawan tsari na gudanar da ayyukan bautar Allah a kasa mai tsarki.