An ba ni kudi don in murde zabe a Jihar Kwara – Kwamishinan Zabe

Kwamishinan Zabe na Jihar Kwara, Malam Garba Madami, ya ce ya ki karbar wasu kudaden da ’yan siyasa suka ba shi a jihar domin ya murde zaben bana da aka gudanar. Madami wanda dan asalin Karamar Hukumar Gurara ne a Jihar  Neja ne ya bayyana haka ne ga manema labarai a Minna bayan auren  ’yarsa. […]

An ba ni kudi don in murde zabe a Jihar Kwara – Kwamishinan Zabe

Farfesa Yakubu Mahmud

Kwamishinan Zabe na Jihar Kwara, Malam Garba Madami, ya ce ya ki karbar wasu kudaden da ’yan siyasa suka ba shi a jihar domin ya murde zaben bana da aka gudanar.

Madami wanda dan asalin Karamar Hukumar Gurara ne a Jihar  Neja ne ya bayyana haka ne ga manema labarai a Minna bayan auren  ’yarsa. Ya ce ya samu matsi daga  ’yan siyasa kan ya karbi kudi, don ya canja sakamakon zabe a Jihar Kwara, amma ya ki amincewa. Ya kara da cewa yanayin aikinsu na zabe wani babban lamari ne, “kuma aiki ne na tsakaninka da Ubangiji ya kamata ka yi abin da ya dace don ci gaban kasa, ko ka jefa kanka a gidan yari,” inji shi.

Ya ce siyasar kudi, da ’yan siyasa ke ganin za su iya sayen al’umma da kudi domin biyan bukatunsu, ba haka lamarin yake ba, “Lamari ne na kare martabarka, saboda haka ya rage gare ka,k a kare mutuncinka. Abin da na yi a Jihar Kwara kafin zabe, shi ne babu wani kudi da za a iya sayena da shi, kuma na sa  jama’a su san cewa kuri’arsu dole ne a kirga su, domin ba ni da niyyar danne hakkin kowa,” inji shi.

Kwamishinan ya ci gaba da cewa shari’oin zabe 765 da aka gabatar gaban kotunan sauraren kararrakin zabe a fadin kasar nan, sun biyo bayan rashin tsarin dimokuradiyya a cikin gidan jam’iyyun siyasar. Ya ce in da jam’iyyun siyasa za su  rika girmama tsarin mulkin jam’iyyunsu ba za a samu matsaloli haka ba.

Yac e Hukumar INEC ita ce mafi ingancin hukuma a fadin kasar nan, saboda yadda aka tsara ta wajen gudanar da ayyukanta.

Madami ya ce babban kalubalensa a Jihar Kwara, shi ne yadda zai sake fasalin ma’aikatan hukumar domin gudanar da ingantaccen aiki. Ya ce ya gode wa Allah ganin yadda ma’aikatansa suke aiki haikan, kuma yana alfahari cewa hukumar ta cimma burinta wajen gudanar da aikinta bisa gaskiya.