An ba Sunday Oliseh shawara
An shawarci sabon Kocin kungiyar kwallon kafa ta kasa wato Mista Sunday Oliseh da ya ba duk ‘yan wasan da ke gida da waje damar gwada kwarewarsu a filin wasa a kokarin da yake na sauke nauyin da aka dora masa na samar da kungiyar da za ta iya karawa da duk takwarorinta a ko’ina […]
An shawarci sabon Kocin kungiyar kwallon kafa ta kasa wato Mista Sunday Oliseh da ya ba duk ‘yan wasan da ke gida da waje damar gwada kwarewarsu a filin wasa a kokarin da yake na sauke nauyin da aka dora masa na samar da kungiyar da za ta iya karawa da duk takwarorinta a ko’ina kuma duk lokacin da suka hadu a filin daga.
Malam Muhammad Garba wani mai nazarin al’amuran wasanni ne ya bayar da wannan shawarar yayin da ya gana da Wakilinmu a Minna ya bayyana cewa,’kuskuren da aka yi ta tabkawa a baya shi ne mayar da ‘yan wasan da ke nan gida ‘yan bora yayin da wadanda ke wasa a kasashen ketare kuma aka mayar da su ‘yan lele wadanda akasari su ake gayyata su yi wa kasar nan wasa a kowane lokaci duk da ba su taka leda yadda ya kamata’.
Malam Muhammad Garba wanda ya yi imanin cewa Allah Ya albarkaci wannan kasar da mutane masu hikima da basira a kowane fanni na rayuwa ya bayyana cewa duk Kocin da ke neman ‘yan wasan da za su yi wa kasar nan wasa yadda ya kamata da kowace kungiya ta duniya za a iya gina su a tsakanin kungiyoyin kwallon kafan da muke da su a duk fadin kasar nan.
Ya yi waiwaye akan marigayi tsohon Kocin kungiyar kwallon kafa ta ’yan kasa da shekara 17 (U-17) Mista Yemi Tella wanda ya zakulo kwararrun matasan ’yan kwallo a kasa da wata shida inda ya tafi da su gasar cin kofin duniya a Kooriya da shekarar 2007 inda suka samu nasarar lashe kofin bayan sun lallasa Sifen a wasan karshe a bugun fanariti.
Da ya juya kan ‘yan wasan kuwa ya shawarce su da su rika sa kishin kasa a duk lokacin suka zo yi wa kasarsu wasa.Ya ja hankalinsu da su san cewa dama ce suka samu wanda wasu ‘yan wasan sun nemi irin wannan damar ba su samu ba.Don haka ya zama wajibi su mayar da hankali su yi wa kasar su wasa da zuciya daya don a samu nasarar da aka sa a gaba.