An ba ’yan Arewa kwana 4 su fice daga wani yankin Jihar Delta

Mun kai shekara 30 muna zaune garin nan, wasu Sakkwatawa wasu Kanawa wasu kuma Katsinawa.

An ba ’yan Arewa kwana 4 su fice daga wani yankin Jihar Delta

An ba al’ummar Arewa wa’adin kwana huɗu su fice daga garin Abavo da ke Jihar Delta.

Fadar Sarkin garin Abavo ta sanar da wa’adin a ranar Litinin, kuma ta ce zai ƙare ne a shekaranjiya Alhamis.

Sarkin Hausawan garin, Usman Alhassan ya ce, ba zato ba tsammani, masarautar ta aiko musu su cewa, “Dole mu bar garinsu, kuma wani ma ba ya da kuɗin motar da zai koma gida.

“Wasu ba su da ma kuɗin cin abinci ballantana na mota, kwana huɗu suka ba mu, daga Litinin zuwa Alhamis,” kamar yadda BBC ta ruwaito shi.

Sarkin Hausawan ya ci gaba da cewa wa’adin barin garin Abaɓo da aka ba ’yan Arewa ya jefa su a cikin tashin hankali.

Ya bayyana cewa yawancinsu sun riga sun tare a Abaɓo tare da matansu da ’ya’yansu, kuma sun fi shekara 30 a garin.

Sarkin ya ce, “Aƙalla Hausawan da ke garin nan sun kai mutum 200, muna sana’ar kayan abinci da nama, wasu kuma leburori ne.”

Ya ce, “Maganar ta zo daga fadar Sarki, yaron sarki ne ya zo ya faɗa mana.

“Mun je domin jin bahasi sai suka ce mana ana sace mutanensu ana neman kuɗin fansa, kuma suna zargin mutanenmu ne,” in ji shi.

Wani ɗan Majalisar Masarautar ya bayyana cewa, “An ɗauki matakin ne saboda yawan garkuwa da mutane don neman kuɗin fansa da ake yi a garin.”

Amma Sarkin Hausawan ya bayyana cewa a iya saninsa da kuma matsayinsa, ba a taɓa kama wani Bahaushe da sunan ya aikata laifi ba.

Ya ce, “Mun kai shekara 30 muna zaune garin nan, wasu Sakkwatawa wasu Kanawa wasu kuma Katsinawa ne wasu kuma ’yan Taraba ne.”

Malam Aliyu Yahya, wanda shi ne Limamin gari na Abavo, ya shaida wa BBC cewa suna faɗi-tashin ganin an samu maslaha.

Limamin ya ƙara da cewa suna ƙoƙarin kwantar wa ’yan Arewa hankali da tare da kira gare su, “Su bi duk hanyoyin da suka kamata domin samun nasara a kan lamarin.”

Liman Aliyu ya ce sanin kowa ne cewa dokar Nijeriya ta ba kowane ɗan ƙasa damar zama a inda yake so ba tare da tsangwama ba.

Kakakin ’Yan sanda Jihar Delta, SP. Bright Edafe, ya ce ba ya da labarin wa’adin da Masarautar garin Abavo ta ba ’yan Arewa.

Ya ce babu wani mahaluki da ke da ikon tayar da wani ɗan Nijeriya daga wani yanki a ƙasar nan ta wannan hanya.